…Gwamna Lawal Ya Bai Wa Ɗalibai 50 Na Jami’ar Crescent Takardun Kammala Karatu
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya miƙa wa ɗalibai 50 takardun shaidar kammala karatu daga Jami’ar Crescent da ke Abeokuta, waɗanda gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin karatunsu a baya.
An gudanar da taron miƙa takardun ne a ranar Alhamis a Babban Zauren Gidan Gwamnati da ke Gusau.
Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa waɗannan ɗalibai sun kammala karatunsu tun shekaru tara da suka wuce, amma suka kasance cikin mawuyacin hali sakamakon rashin biyan kuɗaɗen makaranta daga gwamnatocin da suka gabata.
A cewarsa, Jami’ar Crescent ta ƙi sakin sakamakon ɗaliban ne saboda rashin biyan kuɗaɗen karatun da aka tara tsawon shekaru, lamarin da ya jefa su cikin rashin tabbas da damuwa.
Sanarwar ta ce, bayan gwamnatin Gwamna Lawal ta yi nazari mai zurfi kan lamarin, ta tuntubi jami’ar tare da biyan dukkan basussukan kuɗaɗen karatun da ake bi. Wannan mataki ne da ya bai wa ɗaliban damar karbar sakamakonsu da kuma takardun kammala karatu bayan dogon lokaci suna jira.
Daga cikin ɗaliban 50 da suka amfana, akwai wanda ya samu matakin First Class a fannin Kimiyya (Chemistry), tare da wasu da dama da suka kammala karatu da sakamako mai daraja na Second Class Upper, abin da ya ƙara haskaka ƙwarewa da jajircewar ɗaliban duk da ƙalubalen da suka fuskanta.

Yayin miƙa takardun, Gwamna Lawal ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko ga ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaba. Ya ce wannan mataki ya yi daidai da manufar gwamnatinsa ta ayyana dokar ta-baci a bangaren ilimi, wadda tuni ta fara haifar da sakamako mai kyau.
Gwamnan ya kuma yi kira ga ɗaliban da su yi amfani da damar da suka samu wajen zama jakadu nagari ga jihar Zamfara, tare da bayar da gudunmawa wajen gina ƙasa da al’umma.

A cewar sanarwar, wannan aiki na gwamnan ya ƙara nuna aniyar gwamnatinsa ta gyara kura-kuran da suka faru a baya tare da tabbatar da cewa ɗaliban jihar ba za su sake shiga irin wannan mawuyacin hali ba a gaba.
THESHIELD Garkuwa