Home / Labarai / Dalilin Da Ya Sa Na Gabayar Da Kudiri A Kan Makarantar Harkokin Noma – Aliyu Baffa Misau

Dalilin Da Ya Sa Na Gabayar Da Kudiri A Kan Makarantar Harkokin Noma – Aliyu Baffa Misau

Bashir Bello Majalisar Abuja
Dan majalisar wakilainta tarayya daga Jihar Bauchi Aliyu Baffa Misau ya bayyana kudirin kara inganta harkokin Noma a Najeriya a matsayin hanya mafita da za ta kai kasar ga Tudun tsira.
Da yake tattaunawa da manema labarai Honarabul Aliyu Baffa Misau ya shaidawa manema labaran cewa a halin yanzu an samu yi wa kudirin karatu na farko da na biyu wanda duk ya tsallake su.
Kuma an samu masu ruwa da tsaki domin jin amincewar su ko akasin hakan, dan majalisar ya ce godiya ga Allah madaukakin sarki da har yanzu ba a samu korafin da ke nuni cewa kudirin bai dace ba .
” Dalilan da duka sanya na yi wannan kudirin su ne a tarihin Noma a arewacin Najeriya mazabata na daga cikin wuraren da suka shahara suka yi fice a kan harkar Noma tun kafin zuwan turawa saboda haka har zuwa lokacin mulkin kai. Muna cikin wadanda ke samar da Raken sha wanda kamar yadda muka Sani tun muna yan yara a kan tayar da mota Goma ko Ashirin na rake a rana daya, a Misau mazaba ta aka kawo makarantar Koyar da Noma ta farko a arewacin Najeriya na biyu tun kafin zuwan turawa Najeriya suka gina mana wurin gurzar Auduga kun ga ba za a gina wurin gurzar Auduga ba sai ana da Audugar da za a yi aiki da ita tukunna don haka muna da Dalar Auduga, wurin gurzar Auduga kai ni a matsayina zan iya bugun kirji in ce duk da kudin Gyada da Auduga ne aka gina wuraren mai a Najeriya da iyaye da kakanni suka samar kudin irin wannan arzikin da muke da su ne ta haifar da yin wancan aikin da a shekarar 1983 Gwamnatin tarayya saboda ta san fa’idar Noma a yankin na mazaba ta Misau da Dambam ta samar da wata babbar na’urar da ke Koyar da Noman zamani ta hanyar yin aiki na na’urar zamani ta Injin Noma kuma wannan ya Sanya dukkan Jihohi 19 na Arewa a nan ne ake koya masu don haka muke son a yi makarantar koyar da harkokin Noma ta Gwannatin tarayya Misau kasancewar muna da manya manyan Tafkuna huda biyu da duka hada da Tafkin Diya da Maladumba wanda ko a da can baya idan aka yi maganar gasar Kamun kifi na Arugungu ana maganar Maladumba ne a harkar gasar kamun kifi.
Ya ci gaba da cewa ban da wannan a lokacin da aka kawo Noman Alkama a arewacin Najeriya sai ga shi an zabi Misau daga cikin wuraren da za a yi Noman rani na alkama har yau har gobe akwai ruwa a kasa mai yawan gaske wanda sakamakon hakan mutane kusan ace sun hakuri da Noman Damina sai suka koma Noman rani da ake samun dimbin Shinkafa mai yawa da manyan kamfanoni daga wajen Najeriya ke zuwa  domin samun Shinkafa a nan Misau da Dambam saboda haka da muka tashi yin wannan kudirin mun gayyato masu ruwa da tsaki daga garuruwan kananan hukumomin Misau da Damban da suka tabbatarwa da kwamitin cewa lallai hakika mun cancanci ayi wannan makaranta da babu irin ta a baki dayan Arewa maso Gabas kuma sai dai kawai makarantar tsirai da fulawa ta Gwamnatin tarayya da ke Dadinkowa amma mu a nan muna maganar makarantar Koyar da wadanda za su zama jami’an kula da aikin Gona da dukkan malaman Gona baki daya ta Gwamnatin tarayya kuma kowa ya Sani malaman Gona a Arewa babu su.
Wannan yanki na Arewacin Najeriya maso Yamma jihohin sun hada da Bauchi, Gombe, Adamawa, Yobe da Jihar Borno su suka hadu suka yi shiyyar Arewa maso Yamma don haka lallai mun cancanci ayi mana wannan makaranta ta yadda za a samar da wadataccen abinci a kasa har ma da Makwabta baki daya ta yadda tsaro zai inganta sosai.
Kuma tuni har an tanaji katafaren filin da ya kai hekta dubu biyu da dari biyar (2500) da za a bayar da shi indai za a kawo wannan makarantar da za a rika Koyar da Noman zamani kuma muna da mutane kwararru masana harkar Noma da za su koyar a makarantar idan an yi ta. Kuma bugu da kari Misau kamar wata karamar kasa ce a cikin Najeriya domin babu kabilar da babu a Misau da Dambam suna gudanar da ayyuka, sana’o’insu da sauran harkokin rayuwa.
“Kowa na neman makarantar da ya ga ta dace da shi ne wanda hakan ya sa muma muka nemi wadda ta dace da mu har ma wani kwararre ya ta ba kawo wata magana ta bukatar a hada Makarantar Koyar da Noman zamani ta Misau da muke nema da kuma batun Canjin yanayi akwai yanayin zaizayar kasa ko gurbacewar muhalli da zarar an sa wannan akwai wasu kungiyoyin da za su iya kawo kudin da za a yi bincike a kan ire- iren wadannan.
Ko Gwamnatin jiha ma za ta bayar da gagarumar gudunmawar fili da za ta bayar da takardar shaidar mallaka a fili mai fadin hekta dubu 2500 wanda hakan ba karamar gudunmawa ba ne idan an zo Gwannatin Jiha ta bayar, an kuma san Misau da yin kara idan an zo da wani abu na ci gaban jama’a Gwamnatin Jiha za ta iya cewa za ta gina hanyoyi da wasu ofisoshi ma duk an san mu da wannan karar domin jama’ar kasa su ci gaba kuma gwamna ya tabbatar mana cewa zai sa hannunsa idan mu yan majalisa mun yi na mu aiki na majalisa akwai batun aikin hadin Gwiwa da majalisar tarayya a kan wannan batu, sannan ya ce zai yi magana ta sosai da ministan harkokin Noma kuma in ma har ta kai magana ta je wurin shugaban kasa a Sanya hannu lallai zai ce wurin shugaban kasa ya roki alfarma a Sanya hannu domin wani al’amari ne da zai iya daukar shekaru dari nan gaba bayan ma duk mun wuce jama’a na cin moriyar abin don haka Gwamna na da sha’awa kwarai a kan wannan makaranta don haka ya na dauka tamkar aikin sa ne

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.