Bashir Bello majalisar Habuja
Sanata Garba Musa Maidoki ya bayyana cewa a batun gaskiya koda za a yi dokar yin kiwo a Najeriya ya dace Gwamnati da daukacin al’umma su Sani cewa mafi yawan Shanun da ake da su din ba na Filani ba ne domin na mutane ne da ke cikin gari.
Sanata Garba Musa Maidoki ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja.
” Na ta ba gayawa minista cewa mafi yawan Shanun nan da ake gani ba na Filani ba ne na mutane ne da suke zaune a cikin gari ana dai ba Fulani ne kawai a biya su suna yi wa jama’a kiwo”.
Saboda haka ne muke cewa dole ne Gwamnati ta san dubarar da za ta yi a taimakawa wadanda aka yi wa satar Shanu, “ko dai a ba su Shanu ko kuma wani tallafin da za su mayar da asarar da suka yi saboda batun na cikin harkar samar da tsaro idan an samu wadataccen abinci kuma idan ba a samu abinci ba to, ina batun samar da tsaro?
Maidoki ya ci gaba da cewa da aka kawo batun sai suka ce abin da ya dace a kirkiro wata ma’aikata da za ta kula da bayar da tallafi da kuma bayar da shawara cewa lokacin a rika yin yawo da Shanu ayi nan da can ana bin duk inda aka ga dama ta wuce domin ba ta yadda za a rika yin abin da Kakaninmu sula yi ta fuskar kiwo lamarin ba zai yuwu ba don haka dole ne a kirkiro da hanyoyin zamani na yadda ake kiwon Shanu ana samun amfani sannan kasa ta ci gaba don haka sai muka ga idan an kirkiro da wannan hukuma aka ba ta karfi zai samar da wuraren yin kiwon a wurare wurare daban daban da ke da ruwa da wurin kiwo mai kyau da wadataccen abincin Dabbobi in za a bayar da taimako an san inda za a bayar da shi in kuma Noma masu abinci za a yi an san wurin da za a yi Noman a samu ci gaban da ake bukatar samu.
“Wannan fa kasuwanci ne kuma abinci ne babban batun tsaro na kasa duk kasar da ba ta da shi wato abinci ta shiga Uku, saboda haka muna ganin in Allah ya sa wannan ya samu karbuwa a fadar shugaban kasa bayan an tabbatar da kudirin a majalisa hakika za a samar wa makiyaya taimako. Na gaya masu cewa ni ina da wurin kiwon Dabbobi a nan bayan garin Abuja na gaya wa majalisar Dattawa cewa Shanun gaba daya idan an sayar da su ba su fi miliyan Tamanin ba akwai Awaki, Tumaki duk a ciki, amma ina kashe naira miliyan Casa’in duk shekara kun ga ba amfani amma dai kawai ni Allah ya sa Mani son Noma domin ban iya rabuwa da shi. Don haka ne muke ganin ta yaya Talakawa da ba su da ko miliyan daya zai iya yin wurin kiwon Dabbobi in ba a tallafa masa ba, in kuma ba a taimaka ba, ba ta yadda za a yi a samu wuraren kiwon Dabbobi don haka ya yin haka ne kawai za a samar da hanyar raba fada a tsakani.
” Muna fatan idan mu zo lokacin tabbatar da dokar nan za mu iya kasa ta biyu kashi daya na manyan manoma kashi daya kuma na manyan manoma din haka kowa na da na shi fanni an kuma san irin taimakon da za a ba kowa da irin matsalar da ta damu kowa, ina ganin idan an yi haka za a magance yanayin wani ya samu mai yawa wani bai samu komai ba na tallafin Noma sai dai ina shaidawa jama’a cewa wannan matsalar za a yi maganin ta da yardar Allah