Gidauniyar ADG Care foundation tayi taron karawa juna sani na Mata da nufin samar da guraben kasuwanci ga Mata a Kano ta arewa. Shirin ya horas da mata a kananan hukumomin Kabo da Garo sana’o’i daban-daban domin dogaro da kansu.
Horon da aka gudanar a garin Garo ne da ya hada mata daga sassa daban-daban na karamar hukumar domin koyon sana’o’in hannu da kuma samun tallafi don fara sana’o’insu. Gidauniyar ADG care foundation hadin gwiwa da “Fhuzee, Beyond the Barrier Initiative” domin bada horarwar.
Shirin yana nufin jagorantar Mata a cikin kasuwanci da samar da ƙwararrun mahalarta da jari don fara kasuwancin su, ta yadda za a inganta ƙarfin tattalin arziki.
Shugaban gidauniyar ADG care foundation Injiniya Rabi’u Aliyu Garo ya bayyana cewa sun himmatu wajen ganin sun samar da duk wani horo da dabarun koyawa Mata sana’oin dogaro da kai domin suma su bunkasa sana’o’insu da kuma ba su jari.