Home / Uncategorized / Gidauniyar Bafarawa Ta Taimakawa Mutanen Da Aka Sako Bayan Zanga Zanga Da Kudi Naira Miliyan Shida

Gidauniyar Bafarawa Ta Taimakawa Mutanen Da Aka Sako Bayan Zanga Zanga Da Kudi Naira Miliyan Shida

A kalla kimanin matasan da aka sako bayan kamasu tare da kai su gidan Yari a Abuja inda aka kuma kai su Kotu su 119 ne da aka kama a Jihohin Kano da Kaduna da aka kama lokacin Zanga zangar kalubalantar rashin kyakkyawan shugabanci  da ta gudana.
An dai ba su wannan kudin ne a wajen wani taron da ya gudana a gidan tunawa da marigayi Sardaunan Sakkwato da ke Kaduna.
Bayanan da muka samu na tabbatar da cewa 45 daga cikin wadannan matasan da suka amfana sun fito daga Kaduna ne yayin da kuma 76 sula fito daga Jihar Kano.
Sai dai an bayyana cewa su mutanen Jihar Kano za a ba su na su kudin ne a nan gaba cikin yan kwanaki, kamar dai yadda Darakta Janar na Gidauniyar Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya sanar.
Inda ya ce an bayar da kudin ga matasan ne domin a rage masu radadin wahalar da suka sha a lokacin da aka kama su.
Suleiman Shu’aibu ya ci gaba da bayanin cewa, hakika wannan kokarin da aka yi masu zai taimaka wajen ba su damar ci gaba da iliminsu yayin da kuma wadansu za su fara harkokin kasuwancin ciyar da rayuwarsu gaba ta yadda al’umma za su amfana da su.
“Ba wai ya na goyon bayan irin wannan ba ne illa dai kawai a tausaya masu.
Tsohon Gwamnan na Sakkwato ya bayar da shawara ga matasan da su ci gaba da zama mutanen kirki kuma su rika kiyaye doka da oda a koda yaushe”.
Da yake nasa jawabin mutumin da ya wakilci tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, Malam Abdulrahman Baffa Yola cewa ya yi kowane daga cikin matasan an ba shi kudi naira dubu Hamsin.
Inda ya tabbatar da cewa Zanga zangar tabbatar da an kawai da rashin kyakkyawan shugabanci tsarin ya ga mu da cikas ne sakamakon irin yadda wadansu batagari suka shiga ciki.
“Matasa lallai ya dace su zama masu bin doka da oda musamman wajen ganin an warware matsaloli a koda yaushe”.
Baffa – Yola ya yi kira ga wadanda suka amfana da su yi amfani da kudin kamar yadda ya dace.
Mohammed Abubakar da kuma Abubakar Umar, da suka yi jawabi a madadin sauran wadanda suka amfana duk sun yi wa tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa godiya bisa gagarumin taimakon da ya yi masu.
Wadanda suka amfana dai sun sha alwashin yin amfani da kudin kamar yadda ya dace, kuma sun yi alkawarin ci gaba da zama mutanen kirki tare da ci gaba da gudanar da harkokin iliminsu a dukkan matakai.

About andiya

Check Also

Dangote Hails Tinubu on Impact of Crude for Naira Swap Deal

      …As Dangote Refinery partners MRS to sell PMS at N935 per litre …

Leave a Reply

Your email address will not be published.