Related Articles
Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammed ya nada Alh. Nuhu Ahmad Wabi, a matsayin sabon Sarkin Jama’are wanda Sakataran Gwamnatin (SSG) jihar Bauchi, Barista. Ibrahim Muhammed Kashim, ya wakilta.
A cikin jawabinsa, Barista, Kashim ya ce, yanke shawarar nada Alh. Nuhu Ahmad Wabi an yi ne bisa cancanta tare da yin kira ga al’ummar Jama’are nagari da su marawa Sarkin baya domin ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.
Kafin nadinsa a matsayin sabon Sarkin Jama’are na goma Alh. Nuhu Ahmad Wabi shi ne Yariman Jama’are, (babban dan marigayi sarki Jama’are).
A nasa jawabin sabon sarki Alh. Nuhu Ahmad Wabi ya godewa Gwamna Bala Muhammed da mutanen masarautar Jama’are bisa goyon bayan da suka ba shi tare da yin alkawarin ci gaba da biyayya.
Shugaban karamar hukumar Jama’are Alh. Sama’ila Jarma, ya ce al’ummar Jama’are sun ji dadin nadin sabon sarkin,inda suka ya ba wa Gwamna Bala Muhammed bisa irin kokarin da ya yi wajen baiwa jama’a abin da suke so a masarautar.