Home / Labarai / Gwamna Buni Ya Gabatar Da Kasafin N164bn Ga Majalisar Jihar Yobe

Gwamna Buni Ya Gabatar Da Kasafin N164bn Ga Majalisar Jihar Yobe

 

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

 

 

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni  ya gabatar da kasafin kudi na Naira miliyan 163,155,366,000 ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa a kasafin kudin shekarar 2023.

A cewar Gwamna Buni, an yi wa kasafin kudin lakabin ‘Kasafin kammala ayyuka da inganta tattalin arzikin Jiha’ (Budget of Continuity, Consolidation and Economic Transformation) .

Da yake gabatar da kasafin kudin, Gwamna Buni ya bayyana cewa “kasafin kudin 2023 kasancewarsa na karshe a wa’adin mulkinmu na farko ya ba mu dama mai kyau wajen nuna godiyarmu ga wannan majalisar ta mu mai girma, bisa tsayin daka da fahimtar juna da kyakkyawar hadin gwiwa da Hukumar Zartaswa kan dukkan al’amura dangane da maslahar jama’a.”

“Muna alfahari da wannan mai girma majalisar kuma muna godiya ga dukkan membobin saboda goyon bayan da suka ba mu wanda ya ba mu damar ci gaba da aiwatar da manufofinmu na jama’a game da kula da albarkatu, kiyaye tsarin da ya dace, tabbatar da kyakkyawan darajar kudi, kammala ayyukan da ake ci gaba, samar da kayayyaki na muhimman ababen more rayuwa, farfado da aikin gona, inganta harkokin kasuwanci da habaka kudaden shiga da ake samu, da ci gaba mai dorewa da sauransu”.

Gwamna Buni ya ce, jimillar kasafin kudin aiwatar da manufofinsu da shirye-shiryensu an sanya su ne biliyan dari da sittin da uku, miliyan dari da hamsin da biyar, Naira dubu dari uku da sittin da shida (N163,155,366,000) wanda ke nuni da 0.49.  % raguwa idan aka kwatanta da kasafin kudin 2022.  Kudaden da ake kashewa akai-akai shine za’a kashe Biliyan Tamanin da Bakwai, Miliyan Dari Takwas, Naira Dubu Dari Bakwai da Sha Bakwai (N87,800,717,000) wanda ke wakiltar kashi 57%.

“Kudi biliyan saba’in da biyar da miliyan dari uku da hamsin da hudu da Naira dubu dari shida da arba’in da tara (N75,354,649,000) wanda ya nuna kashi 43% an ware su ne domin kashe kudi.

Da yake karin haske kan kasafin kudin, Buni ya bayyana cewa, “kasafin kudin 2023 zai tsaya kan kammala ayyukan da ake gudanarwa a kokarin gwamnati na farfado da tattalin arzikin kasar bayan tashe-tashen hankula da jihar ta yi fama da shi.

“Saboda haka, za mu mai da hankali kan abubuwa masu zuwa, amma ba a iyakance ga masu zuwa ba Gwamnati za ta ci gaba da kokarinta na gina tituna a matsayin babban abin da ya shafi ci gaban ababen more rayuwa don isar da kayayyaki da ayyuka yadda ya kamata don jawo hankalin masu zuba jari na gida da na waje.

Gwamnan ya kuma yi albishir ga dukannin mutanen da suka samu sababbin gidajen da gwamnatin ta gina da cewar, gwamnatin ta musu rangwame da kashi 50% cikin dari.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.