Home / Labarai / Gwamna Ganduje Ya Amince Za A Yi Muqabala Tsakanin AbdulJabbar Sheikh Nasiru Kabara Da Malaman Kano

Gwamna Ganduje Ya Amince Za A Yi Muqabala Tsakanin AbdulJabbar Sheikh Nasiru Kabara Da Malaman Kano

Gwamna Ganduje Ya Amince Za A Yi Muqabala Tsakanin AbdulJabbar Sheikh Nasiru Kabara Da Malaman Kano

 

 

Sakamakon wani zama na musamman da Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi da malamai na dukkan bangarori, gwamnan ya amince za a yi Muqabala tsakanin AbdulJabbar Sheikh Nasiru Kabara da kuma malaman jihar Kano na dukkan bangarorin Musulunci nan ba da jimawa ba.

 

 

 

Bayanin hakan na kunshe a cikin wata takardar sanarwa mai dauke da sa hannun Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano da aka rabawa manema labarai, takardar ta ci gaba da bayanin cewa.

 

 

Bayan an yi mitin din, an cimma matsaya wacce gwamnan ya amince da dukkan abubuwan da a ka cimma. Daga cikin wadanda suke wajen mitin din bayan su malaman, da akwai Kwamishinan Harkokin Addini, Dr Muhamad Tahar Adam da kuma Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jiha, Aramma Ali Haruna Makoda da kuma tsohon dan takarar Gwamnan jihar Kano, Malam Saluhu Sagir Takai.

 

 

An amince da cewar za a hada Muqabala wacce za a nemi AbduJabbar ya kawo da’awarsa saboda Malamai su yi mata filla-filla a faifai. Kuma za a jona Muqabalar kai tsaye da dukkan gidajen rediyo na cikin gida da kuma na waje.

 

 

An amince cewar a wannan Muqabala dukkan bangarorin Malaman Musulunci za su kawo wakilansu. Sannan kuma za a gayyaci wasu mashahuran Malamai daga wajen jihar Kano, su zo su gani da idonsu yadda Muqabalar za ta kaya.

 

 

Gwamnatin ce za ta bayar da wurin da za a yi wannan Muqabala. Sannan kuma za ta samar da dukkan tsaron da ya dace da yanayin. Za a tabbatar da tsaro lokacin Muqabalar da kuma bayan an kammala Muqabalar.

 

 

An nemi Malaman da za a yi wannan Muqabala da su, da su je su shirya hujjojinsu nan da sati biyu. Cikin kokarinsu na fuskantar AbdulJabbar din lokacin wannan Muqabala ta tantance aya da tsakuwa.

 

 

Gwamna Ganduje ya amince da wannan maganar ta Muqabala ne saboda a ba AbdulJabbar hakkin sauraronsa kamar yadda ya nema. Ya kuma nemi da jama’a su kwantar da hankalinsu lokacin da za ai wannan Muqabala da kuma bayan an gama Muqabalar.

 

 

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.