Related Articles
Daga Imrana Abdullahi, Kaduna
Gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya ya sake nada sabbin mashawarta na musamman.
Wata sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun sakataren din – din -din na gidan gwamnatin Jihar Gombe, Balarabe Poloma, ta bayyana Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi a matsayin sakataren gwamnatin jihar (SSG), yayin da Ismaila Uba Misilli aka nada shi babban darakta a harkokin siyasa.
Haka kuma a cikin jerin sunayen akwai Dokta.Mu’azu Shehu wanda zai sa ido a kan Bincike da takardu a matsayin Darakta Janar