Gwamna Zulum Ya Ziyarci Asibiti, Ya Tabbatar Da Mutuwar 10,47 Sun Samu Raunuka
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Borno Furofesa Babagana Umara Zulum ya tabbatar da salwantar rayukan mutane 10 kuma mutane 47 sun samu raunuka sakamakon harin da yan Boko Haram suka kai da makaman rika a unguwar Gwange.
Gwamna Zulum ya bayar da tabbacin cewa Gwamnati na daukar matakan tsaro, inda ya bayar da tabbacin cewa yan Ta’adda ba za su sake samun iko da Marte ba.
Gwamnan dai ya ziyarci asibitoci guda biyu ne a ranar Laraba, bayan da mayakan Boko Haram suka kai harin wuta da makaman Roka masu tarwatsewa a duk inda suka sauka, inda sanadiyyar hakan suka kashe mutane 10 wasu 47 kuma suka samu raunuka a garin Maiduguri.
An dai ji karar harbe harbe a daren ranar Talata daga unguwar bayan gari ta Kaleri, a bayan birnin Jihar Borno na Maiduguri, wanda daga nan ne aka samu bayanin tafiyar makaman Roka masu fashewa sun fada a Unguwar Gwange da Adam Kolo dukkan wuraren kuma cike suke da mutane a cikin birnin Maiduguri. Mafi yawan mutanen da suka mutu a cikin birnin Maiduguri ne a unguwar Gwange. Daya daga cikin makaman da aka harba suka fada a wurin da yara suke wasa a unguwar Gwange, kamar yadda aka tattara bayanai.
Gwamnan Jihar Borno Zulum ya tabbatar da kai harin lokacin da ya ziyarci asibitin kwararru da kuma asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri. An kuma shaidawa Gwamnan cewa wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su duk sun samu raunuka daban daban kuma tuni an rigaya an duba su, inda nan take Gwamnan ya bayar da umarnin cewa ma’aikatar lafiya ce za ta biya kudin maganin da aka yi masu.
“Hakika wannan abin bakin ciki ne ga mutanen Jihar Borno wannan lokacin inda lamarin ya shafi mutane 60 saga cikinsu har 10 sun riga mu gidan gaskiya. Kuma hakan ya faru ne sakamakon irin yadda maharan suka harba makamai daga nesa. Ina mai imanin cewa wannan sabon salon yaki ne kuma dole ne mu tashi tsaye domin ganin bayansa. Mun ta ba samun wani abu makamancin hakan a shekara daya da ta gabata. Wato Mafitar shi ne mu samar da wani tsari na kimiyya,wanda zamu yi aiki a kansa. Hakika na ji zafin faruwar wanann lamari, don haka ba wai mun ziyarci asibitin kawai ba ne,Mun yi aiki sosai a tsakanin jami’an tsaro masu yaki da matsalar Boko Haram kuma za mu ci gaba da yin hakan tare da Sanya kwazo sosai”, inji Zulum.
Da yake jawabi a game da nasarar sake dawowa da Marte, da yan Ta’adda suka kwace yan kwanakin baya da suka gabata, Gwamna Zulum ya ce ba wai yana fadin mai yuwuwa ba ne a’ a ya tabbata cewa sojojin Nijeriya Nijeriya za su tabbatar da hakan domin suna aiki ba dare ba rana, haka kuma za su ci gaba da aikinsu na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin jama’a tare da yin hani ga duk wani ko wasu gungun yan Ta’adda daga kasa samun iko da Marte kuma nan gaba.
“Ina bayar da tabbacin cewa yan Ta’adda ba za su sake samun iko da garin Marte ba”, Inji Zulum.