Daga Imrana Abdullahi
A wani kokarin kara fadakar da dimbin yayan jam’iyyar PDP mutumin da ya tsayawa jam’iyyar takarar shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya tabbatar wa da mambobin majalisar wakilai ta kasa cewa kowa ya dace ya Sani cewa Gwnatin Tinubu ta wuccin Gadi ce.
Atiku Abubakar ya ce zai kwato mukamin shugaban kasa daga wurin Bola Tinubu ta hanyar yin amfani da samun hukuncin kotu
“Atiku ya kuma bayyana gwamnatin Tinubu a matsayin na wucin gadi, inda ya kara da cewa an samu hakan ne ta hanyar yin amfani da tafka magudin Zabe”.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP na zababbun jami’an jam’iyyar a jihar Bauchi da ya gudana a ranar Asabar.
“Gwamnatin PDP ta fara cire tallafin a matakai 2 bayan ta samar da kayan jin dadi”, inji
A cewar Atiku, “Kuna nan ne domin ku kasance masu adawa da wannan gwamnatin ta wucin gadi.
“Bisa sakamakon da hukumar zabe ta INEC ta bayyana da kuma jiran tantance kalubalen zabe a kotu, mambobinmu ba su ne mafi rinjaye a majalisar dokokin kasar ba.
“Don haka, a halin yanzu, dole ne su shirya yin aiki a matsayin adawa mai inganci, tare da yin shiri don yuwuwar rawar da mafi yawan jam’iyya za ta iya takawa idan an