Daga Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Zamfara ta fara wani gyara na musamman na wayar da kan jama’a da nufin magance matsalolin kiwon lafiya da inganta rayuwar al’umma.
Kashi na farko na shirin wayar da kan likitocin tare da hadin gwiwar ofishin uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal an tsara shi ne don bayar da aikin jinya kyauta ga mutanen da suka kamu da cutar da ke bukatar a duba masu ido, kumburin hanji (hernias, hydroceles), vesicovaginal fistula da batutuwa a kan Yoyon fitsari (VVF), da ilimin kiwon lafiya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ta bayyana cewa, aikin da aka yi na wayar da kan jama’a da aka fara a ranar Juma’ar da ta gabata, an yi maganin batutuwan ido guda 81 da kuma wasu 49 na kumburin hanjin.
Ya kara da cewa an tsara wannan shiri na musamman domin daukar nauyin marasa lafiya 1,000 da ke fama da kumburin hanji a kowane wata, da gyaran yoyon fitsari (VVF) guda 200, da kuma majinyata 1,000 da ke fama da ciwon ido.
Sanarwar ta kara da cewa: “Gwamnatin jihar Zamfara ta kafa kwamitin kwararru da suka gudanar da tantance cibiyoyin yi wa jama’a hidima a jihar domin gano matsalolin fida da suka zama ruwan dare ga al’umma.
“Bisa binciken da ya gudanar, kwamitin ya gano cire ido, kumburin hanji (hernias, hydroceles), gyare-gyaren yoyon fitsari (VVF), da ilimin kiwon lafiya a matsayin wuraren fara shiga tsakani na shekarar farko ta shirin.
“Wannan shi ne irinsa na farko a tarihin Zamfara, da gwamnatin jihar ke gudanar da aikin ba da jinya kyauta wanda ya shafi irin wadannan muhimman wurare.
“Aikin wayar da kan jama’a na amfani da wayar tarho ga majinyata daga yankunan karkara da kananan birane domin ba da kulawa ta musamman ga mabukata.
“An yi amfani da dabarar da za ta ba da damar duba marasa lafiya daga nesa, sannan a rika karbar magani a wuraren da aka kebe a Gusau.
Kwamitin ya kuma ziyarci hukumar kula da magunguna da kayayyakin masarufi (DMCMA) da ke Gusau tare da kwarin gwiwar samar da kayayyakin da ake bukata don shirin wayar da kan jama’a.
“A cikin kudurinsa na farfado da fannin lafiya da kuma tausayi, Gwamna Dauda Lawal ya kara fadada tsarin shirin da ya shafi dukkan kananan hukumomi 14 na jihar. Cibiyoyin wayar da kan jama’a sun hada da Babban Asibitin Gusau, Babban Asibitin Sarki Fahad, da Asibitin kwararru na Yariman Bakura. Dukkan shari’o’i na musamman za a tura su zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Gusau.”