Related Articles
Daga Bashir Bello Abuja
Sanata Babangida Husaini, Mai wakiltar yankin Jigawa ta Arewa maso Yamma ya bayyana batun jarabawar hadarin Tankar mai da ya faru a kauyen Majiya a Jihar Jigawa da cewa lamarin da ya faru abu ne mai tayar da hankali kwarai matuka.
” labarin da ya zo mana shi ne motar mai ce bodin ya Kwabe daga kan motar kuma ya na zubar da mai, amma a sanadiyyar irin halin da ake ciki ya dace ma’aikata su hana kowa kusantar motar domin zubar da Man ke yi amma ba a samu hakan ba har mutane suka rika dibar mai garin dibar man har wuta ta tashi.
Kuma abin takaici mutane sun kai dari wadansu a wurin suke wasu kuma wutar ce ta tarar da su wasu a kan baburansu wasu na wurin sana’ar Shayi da masu sayar da Nama haka dai motar ta yi bindiga har ta fantsama ta tarar da su sai wuta ta tashi da a yanzu haka mutum sun kai dari shida da suke asibitoci daban daban asibitin Mai Gemuasibitin Gumel, asibitun Jahun , Birnin Kudu da Hadeja ana ta ceton rayuwarsu saboda tsananin raunin da suka samu.
Sanata Babangida ya kara da cewa ya gabatar da kudirori a gaban majalisar Dattawa kamar kuda Uku na farko a tashi ayi masu addu’a saboda wasu sun rasu kuma da addu’a ga marasa lafiya Allah ya ba su lafiya sai na biyu neman taimakon gaggawa daga Ma’aikatun Gwamnati a kwai ma’aikatar Jinkai akwai hukumar bayar da tallafin gaggawa ta kasa NEMA sai kudiri na Uku wato jawo hankalin ma’aikata na tsaro musamman masu kula wa da hadari da abin da ya shafi hanya da a tabbatar mutane ba su kai ga inda abin ya faru ba kuma a tabbatar an kawo taimakon da zai yi maganin hakan.
” A magana ta gaskiya akwai rashin sanin irin hadarin abin da zai iya faruwa ko hadarinsa wadansu ba sa sanin hadarin Fetur ko Gas haka zaka ga idanunsu a rufe kawai sun shiga wasu kuma kuskure ne da bama fata lamarin ya faru ba wai yankina ba a ko’ina ba ma fatan ya faru kuma duk majalisa ta Karbe su an kuma bayar da izinin gaggawa a kai masu tallafi da wuri.
Sai kuma ya yi kira ga Malamai da Sarakuna a rika fadakarwa ga jama’a kuma a karfafa dukkan wadannan bangarorin sai kuma iyaye su rika zaunar da yaransu su rika gaya masu hadarurrukan iron wadannan abubuwa domin yawancin wadanda abin ya shafa yawanci yara ne kanana da Mata wasu wutar tarar da su ta yi wasu kuma yara ne garin kallo domin ba su san illar abin ba sai abin ya faru gare su.
“Gwamna Malam Umar Namadi da shi aka yi Jana’izar bayin Allan nan kuma da irin tsarin Gwamnatinsa da sanin da muka yi masa mun san ba zai yi kasa a Gwiwa ba mun san zai kai tallafi. Mun kuma yi magana da shugaban karamar hukumar Taura ya kuma tabbatar mana cewa ana kididdigar wadanda abin ya shafa na asibitoci da wadanda suke a guda har ma da wadanda suka rasu kuma ya tabbata Mani cewa za su fara kai tallafin daga yau. Babban lamari dai shi ne majalisa ta Sani da Ma’aikatun Gwamnati kuma duk sun Sani shi ne muhimmin abu za kuma muga in mun koma gida me za mu iya yi da abin da kowa irin gudunmawar da zai bayar.
Sanatan ya kuma aika sako ga matasa da du kiyaye da irin wannan da kuma tarbiyya iyaye sai sun bayar kuma gwamnati ma sai ta bayar kullum kiran mu a garesu a kiyaye mummunan aiki akama aiki nagari damuwarmu a samu ilimi nagari jama’a su zama mutane nagari kamar yadda mu iyaye suka yi mana tarbiyya don haka kira na a garsu shi ne don Allah a gujewa suk abin da baya kan ka’ida don kar rayuwa ta kasance a cikin hadari, kamar yadda a la san halin Hausawa yan Arewa da biyayya ga iyaye da gwamnati da tsare dokokin addini idan an ga mota ta fadi a bar ma’aikata da ke da hakkin yin aikinsu duk abin da ya shafi batun Mai ko wani abu mai hadari batun zuwa kallo ma bai ko taso ba