By Rabiu Sanusi
Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabun Kiru da Bebeji a majalisar tarayya Rt Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa,(PhD)a ya shirya taron addu’o’i tare da bada tallafi a mazabun da yake wakilta.
Hon Kofa ya shirya taron ne musamman wanda ya haɗa sama da mutum 10,000 domin yin addu’o’i a garinsa na Kofa da ke Karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano.
Ɗan majalisar mai hawa huɗu ya shirya taron ne Dan nuna godiyar sa ga Allah saboda nasarar da ya samu a Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe da ta Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja a makwon da ya gabata,tare da raba wa su kayan tallafi ga ’yan mazabar sa.
A lokacin da aka shirya kasaitaccen taron dai,an bayar da tallafi ga ’yan mazabar su 10,000 maza da mata. Bugu da ƙari, an ba mutanen tallafin kuɗi da kayan sana’a da motoci da kayan abinci da suttura da kuma sauran kayan amfanin yau da kullum.
Kazalika,an yi addu’a ta musamman ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, domin neman Allah Ya ba shi nasara a Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta Ƙoli, da sauran ’yan majalisar Kano na NNPP da suka yi nasara a kotu.
Sannan Kuma yayi fatan nasara ga waɗanda ba a kai ga yanke na su hukuncin ba,Sannan an yi wa jagoran Ɗariƙar Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, addu’ar neman Allah Ya ja kwanan sa, Ya ƙara masa lafiya da kuma biya masa bukatunsa.