Home / Uncategorized / Ina Jinjinawa Tinubu, Matawalle Da Dukkan Sojojin Najeriya

Ina Jinjinawa Tinubu, Matawalle Da Dukkan Sojojin Najeriya

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinlafi, Sarkin Shanun Shinkafi na farko ya bayyana Yabo da jinjina ga ministan kasa a ma’aikatar tsaron Najeriya Dokta Muhammad Bello Matawalle, shugabannin rundunonin Sojojin Najeriya da dungurungum shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bisa irin yadda suka kaiwa al’ummar Shinkafi daukin maganin matsalar tsaron da suka shiga ciki.

Dokta Suleiman Shinkafi ya ce hakika wadannan gwarzon shugabanni sun cancanci a yaba masu tare yi masu jinjina mai karfi sakamakon jarunta da nuna wa al’ummar karamar hukumar Shinkafi gata da kuma hanzarin fitar  da su a cikin matsalar da suke ciki.

“Akwai wata bajintar da jami’an tsaro suka yi wa jama’ar karamar hukumar Shinkafi na kama wadansu mutanen da ake zargin cewa suna yi wa yan Ta’adda aikin bayar da bayanai ana cutar da jama’ar da ba su ji ba ba su gani ba, hakika a wannan karamar hukuma an kama wadansu muhimman mutanen da ba a yi tsammani ba don haka muka kara yin kira ga jami’an tsaro da kada su yi kasa a Gwiwa duk wanda suka kama lallai su tabbatar da an yi masa hukunci na kwarai domin yan baya da dukkan sauran al’ummar Najeriya kowa ya shiga cikin taitayinsa”, inji Dokta Suleiman Shinkafi.

“Ni a matsayina na mutumin da aka haifa a cikin garin Shinkafi ina jinjinawa sojojin Najeriya kwarai bisa jajircewar aikin da suke yi a halin yanzu, ina kuma yin kira ga daukacin al’ummar kananan hukumomin Shinkafi da Zurmi da kuma Jihar Zamfara, Arewacin Najeriya da na kasa baki daya da suka kara matsa kaimin wajen yin addu’o’in Allah ya kawar mana da duk wata matsalar rashin tsaro baki daya Allah ka amintar da mu a koda yaushe mu kasance cikin Aminci da salama ba tare da duk wani nau’in tashin hankali ba”.

Kuma ina yin kira ga jama’a da a ciki gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga jami’an tsaro domin su ci gaba da gudanar da ayyukansu a kowane lungu da sako na Shinkafi, Jihar Zamfara da kasa baki daya.

Ina tabbatarwa da jama’a cewa Burin Matawalle samar da cikakken ingantaccen zaman lafiya da karuwar arzikin jama’a baki daya

About andiya

Check Also

Call Your Wife To Order, Niger Delta Groups Warn Uduaghan, Husband Of Senator Natasha

    ..Say outburst against Senate President Akpabio, shameful, unwomanly A coalition of groups from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.