Home / Big News / Jaridar NEW TELEGRAPH Ta Karrama Gwamna Lawal Da Lambar Yabo Ta Gwamna Mafi Nagarta Na Shekarar 2025

Jaridar NEW TELEGRAPH Ta Karrama Gwamna Lawal Da Lambar Yabo Ta Gwamna Mafi Nagarta Na Shekarar 2025

 

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu lambar yabo ta Gwamna Mafi Nagarta na Shekarar 2025 daga jaridar New Telegraph, saboda fitattun ayyukan sa na ci gaba a jihar.

Gwamnan ya karɓi wannan lambar yabo ne a ranar Juma’a, yayin bikin raba lambobin yabo da liyafar dare da jaridar ta shirya a babban ɗakin taro na Lagos Oriental Hotel.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa jaridar ta girmama Gwamna Lawal ne saboda muhimman ayyukankawo sauyi da gwamnatinsa ke gudanarwa a muhimman sassa na jihar Zamfara.

Ya ce, “Jaridar New Telegraph ta naɗa Gwamna Dauda Lawal a matsayin Gwamna Mafi Nagarta na shekara ta 2025 saboda ayyukansa.

“Lambar yabo, wacce Hukumar Editoci ta Daily Telegraph Publishing Company ta bayar, ta gano yadda gwamnan da gwamnatinsa ke aiwatar da manyan sauye-sauye da ayyuka a fannoni kamar ilimi, gyaran birane, da samar da manyan abubuwan more rayuwa, domin inganta rayuwar al’umma da bunƙasa cigaba mai ɗorewa a jihar.

“Jaridar ta kuma jero wasu dalilan karramawa, ciki har da ƙoƙarin gwamnan na magance matsalar bashin ma’aikatan gwamnati da suka daɗe har tsawon shekaru 13 na dala miliyan 16, da kuma biyan kuɗin WAEC da NECO da aka bari fiye da shekaru uku, da sauran ayyuka masu muhimmanci.”

Yayin da yake karɓar lambar yabo, Gwamna Lawal ya gode wa hukumar gudanarwa da Hukumar Editoci ta Daily Telegraph kan ganin ya cancanci wannan girmamawa.

Ya ce, “Wannan karramawa tana ƙara min kwarin gwiwa da zai motsa ni da gwamnati na mu ƙara himma wajen aiwatar da ƙarin ayyuka da tsare-tsare domin amfanin jama’a a jihar Zamfara.”

About andiya

Check Also

Gwamna Lawal Ya Lashe Kyautar Gwarzon Gwamnan Shekara Ta Jaridar LEADERSHIP, Ya Sake Jaddada Ƙudirin Ci Gaban Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake tabbatar da ƙudirin gwamnatin sa na kawo …

Leave a Reply

Your email address will not be published.