Home / Labarai / KADA MA’AIKATA SU ZABI MASU KUNTATA MASU – SAKATARIYA CHRISTIANA

KADA MA’AIKATA SU ZABI MASU KUNTATA MASU – SAKATARIYA CHRISTIANA

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI

 

 

An bayyana taron fadakarwa ga ma’aikata da cewa saka ce da aka fara da kyakkyawan Zare.

Bayanin hakan ya biyo bayan irin taron fadakarwar da Kungiyar Kwadago ta NLC ta fara yi ne a Jihar Kaduna arewacin tarayyar Najeriya.

Sakatariyar kungiyar Christiana John Bawa ta bayyana cewa sun shirya wannan taron fadakarwa ne domin ma’aikata su samu damar tantance duk wani mai son tsayawa takara su tabbatar da ya dace a zabe shi ko kuma.

Christiana John Bawa ta bayyana hakan ne a lokacin da take ganawa da manema labarai a Kaduna.

“Muna son shiga cikin harkokin siyasa musamman ma’aikata su tsaya takarar neman Kujerun yan majalisar Jiha, Tarayya, majalisar Dattawa da Gwamnoni saboda kare mutunci da martabar ma’aika domin idan an samu wani da ke son yin wata dokar da za ta kuntatawa ma’aikata su ce ba su yarda ba da dokar ba sam.

Christiana ta ci gaba da bayanin cewa ” akwai wasu Jihohi a Najeriya da har yau ba su iya biyan sabon tsarin albashin ma’aikata ba kuma mu na ganin Gwamnonin nasu na fita za su yi takarar shugaban kasa duk da halin da Jihohinsu ke ciki, ya dace jama’a fa su du ba idan kana matsayin Gwamna baka ba ma’aikaci hakkinsa ba sai ka zama shugaban kasa ne zaka bashi? Kuma idan kana Gwamna ka Kori ma’aikata baka ba su kudin fansho da ko kudin sallama ba sai ka zama shugaban kasa ne zaka bashi? Kai akwai ma wadansu Jihohi da dama da ba su karbi albashin watanni da dama ba saboda haka irin wadannan kowa ya Sani idan sun yi shugaban kasa Najeriya za ta mutu”.

Saboda haka muke yin kira ga ma’aikata da su bude idanuwansu kuma su rika jin labarai a rediyo, jaridu da kuma Talbijin domin su San abin da ake ciki.

Saboda haka ina kira ga jama’a da su tabbata duk mai irin wannan in sun tsaya zabe kada su zabe su ko dan majalisa ko wane irin zabe suka tsaya kar su zabe su, koda batun zaben fitar da dan takara ma kada su bari su samu, a zabi wadanda ke da kishin ma’aikata ba irin masu gudun ma’aikata ba akwai kuma wasu da idan an zabe su ba za a kara ganin su ba sai shi kenan don haka irin wadannan mutanen muke yin kira ga ma’aikata da su tabbatar ba su zabe su ba ko kuma su dawo kan kujerunsu”. Inji Christiana.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.