Daga Bashir Bello, Majalisa Abuja.
Dan Majalisar Datttawa mai Wakiltar mazabar Barno ta Kudu Sanata Ali Ndume, wanda shi ne mai tsawatarwa da ake yi wa lakabi da Bulaliyar Majalisa Dattawa ya nuna gamsuwarsa da hujjojin da Shugaban Kasa Ahmed Tinubu ya gabatar masu na ciyo bashin in da ya ce ba laifi bane ciyo bashi sai dai bashin ayi amfani da shi wajen aiwatar da aiyuka da za su kawo ci gaban kasa wannan ne abin da yake fatan gani a yi wa kasa da jama’arta aiki kawai.
Game da kasafin kudi da Majalisar ta amince da shi na samar da Naira Tiriliyan biyu kuwa, Sanata Ndume ya ce sun amince da shi ne, saboda mafi yawan kasafin kudin za a yi amfani da shi ne wajen inganta rayuwar yan Najeriya.
Ya ce daga cikin kudin za a yi amfani da shi ne wajen bayar da tallafi ga talakawa mutum miliyan 15 da Karin albashin ma’aita da kuma samar da karin yawan sojoji da kayan aiki da Karin albashin Yan sanda da harkar noma da gyaran hanyoyi da sauran su.
Sanata Ndume ya ce cece- kucen da ake yi a kan sayen motoci ga fadar shugaban kasa na Naira Biliyan 28 kawai kuma akwai bukatar motoci a gidan ne kuma ba Bola Ahmed Tinubu za a sayawa ba, fadar za’a sayawa koda ya ta fi za a ci gaba da amfani da su a fadar ta shugaban kasa.
Sanatan ya yi alkawarin cewa Majalisar Dattawa za ta saka ido wajen ganin ayyukan da aka ce za a yi da kudin an yi amfani da su kamar yadda ya kamata idan kuma ba a yi ba za su sanar da Yan Najeriya rahoton binciken.