Home / Labarai / Kasa Daya Al’umma Daya Ce Mafita A Nijeriya – Denham

Kasa Daya Al’umma Daya Ce Mafita A Nijeriya – Denham

Kasa Daya Al’umma Daya Ce Mafita A Nijeriya – Denham
Mustapha Imrana Abdullahi
Mista Julius Denham, shugaban kungiyar da ke kokarin fadakar da jama’a muhimmancin zaman tare a kasa daya al’umma daya ba tare da samun wani bambanci ba tsakanin Juna, ya tabbatarwa manema labarai cewa tsayawa tare da Juna ne mafita a Nijeriya.
Ya bayyana hakan ne lokacin da ya kawo ziyara ga cibiyar yan jarida ta kasa reshen Jihar Kaduna, inda ya ce hakika abin da Nijeriya ke bukata a halin yanzu shi ne a taru wuri daya tsakanin masu yawan shekaru da kuma matasa domin lalubo mafita a Nijeriya.
“Hakika muna bukatar zaman tare domin Nijeriya Nijeriya wai ta na bukatar masu yawan shekaru ba ne su zama shugabanni ko kuma masu karancin shekaru wato matasa ba ne su zama shugabanni a Nijeriya, duk ana bukatar dukkan bangarorin biyu ne su hada kai ayi aiki tare domin samun ingantacciyar kasa”, inji Denham.
Julius Denham ya kara da bayanin cewa wannan fadakarwa kan cewa “ni dan Nijeriya ne” sun yi nisa da shi saboda a halin yanzu sun samu nasarar bude manyan Ofisoshi a Jihohi 16 a fadin tarayyar Nijeriya don haka muna kokarin fadakar da kowa ya kasance ya shigo cikin wannan fadakarwa.
“Mun samu nasarar ganawa da manyan mutane a Nijeriya da suka hada da Gwamnoni da yan siyasa da kumadimbin muhimman mutane da yawa duk a kan wannan fadakarwar ta kowa ya zama dan kishin kasa, idan kaje kasar Amurka a halin yanzu da ka tambayi kowane Ba- Amurke ba zai gaya maka cewa shi dan yanki kaza ko kaza ba ne kawai shin dan Amurka ne kawai shikenan ba wata magana, sabanin halin da aka saka Nijeriya a ciki da ya sha bamban da yadda lamarin yake a can baya ba babu wani nuna bambancin bangaranci, yanki ko kabila kowa daya ne kawai”, inji Denham.
A nasa jawabin Shugaban Kungiyar yan jarida ta kasa reshen Jihar Kaduna Kwamared Adamu Yusuf, matsalar Nijeriya ita ce ta rashin kishin kasa.

“Hadama da rashin Kaunar juna ya yi yawa a kasar nan mutum daya sai ya kwashe dukiyar da za ta wadaci al’umma da yawa amma sai ya kwashe komai shi kadai”.
Ya ci gaba da cewa ziyarar da wannan kungiya ta fadakarwa a ge da cewa ni dan Nijeriya ne ta kara fadakar da daukacin yan jarida baki daya.
“Mutum ba zai san cewa kasar nan Allah ya albarkace mu da wadata iri iri ba sai mutum ya ziyarci wadansu kasashe a duniya”, inji Yusuf.
Kwamared Adamu Yusuf ya ci gaba da bayanin cewa idan mutum ya je wadansu kasashe zai ga a Nijeriya akwai sauki, sabanin yadda farashi da rayuwa take a wadansu kasashen duniya.
” Da naje kasar Saudiyya Ayaba kwara uku kawai naira dubu daya kuma haka abin yake a sauran farashin kayayyaki, wanda a Nijeriya za ta iya sayen Ayaba baki daya naira dari biyar zuwa dari shida”, inji kwamared Adamu Yusuf.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.