Kungiyar Kwallon Kafa Ta Amana Fc Rigachikun Ta Lashe Gasar Kwallon Kafa Ta Gwamna Sanata Uba Sani karo Na 6 Domin Zaman Lafiya
Kamar yadda Honarabul Barista Ibrahim Bello Zero ya aiko mana da irin yadda gasar kwallon kafa da ya Sanya wa kungiyoyin kwallon kafa domin zaman lafiya a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa.
An dai buga wannan gasar kwallon kafa ne ta karshe a makarantar Firamare Malam Jallo Rigachikun da ke cikin garin Kaduna.
An dai yi wannan gasar kwallon kafa ne tsakanin kungiyoyin kwallon kafa ta Amana DC Rigachikun da kungiyar kwallon kafa ta Marabar Jos Academy.
Kungiyar kwallon kafa ta Amana fc Rigachikun ta lashe gasar.