Home / Ilimi / Kungiyar Tsofaffin Daliban Kaduna Poly Sun Tallafawa Mutanensu

Kungiyar Tsofaffin Daliban Kaduna Poly Sun Tallafawa Mutanensu

 Daga Dattijo Abdullahi
Kungiyar tsofaffin daliban makarantar kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna sun Tallafawa wasu daga cikin tsofaffin daliban da kayan abinci domin rage masu radadin zaman gida da ake ciki sakamakon cutar Korona bairus.
Da yake jawabi a wajen taron rabon kayan abincin da aka rabawa mutane 105 shugaban kungiyar Alhaji Abba Anas Adamu ya bayyana cewa bisa la’akari da irin halin da duniya take ciki ne yasa suka ga dacewar su tashi tsaye domin nemowa mutanensu dan abin da za su rage radadin zaman gida da shi.
Wannan shi me hoton yadda aka nunawa jama’a irin yadda yakamata su wanke hannu, bayar da tazara tsakanin Juna da Sanya abin rufe baki da hanci domin kariya.
“Hakika mun yi la’akari da irin halin da ake ciki na radadin zaman gida ne yasa muka rubutawa wadansu takardun neman su taimaka domin wasu daga cikin mambobin kungiyar har ma da wadanda suka kammala makarantar amma ba su yi rajista ba duk suna neman taimako domin halin rashin fita a nemi abinci ya tsananta kwarai”.
Samfurin yadda aka ba mata wannan Tallafi kenan a lokacin taron
Shi yasa muka rubutawa wadansu hukumomi musamman masu zaman kansu domin su agaza kuma wadansu sun taimaka shi yasa muka ga ya dace mu kira wadanda aka san suna bukatar wannan tallafin mu fara yin kashi na farko da su, my ba su ko dai yaya yake kadan ya fi babu.
Ga hoton mutanen da suka amfana nan lokacin da shugaban kungiyar ke yi masu jawabi
“Muna kuma saran nan gaba kadan zamu ci gaba da aiwatar da wannan Tallafi, saboda a yanzu mun Nemo wadanda kodai ba su da abin yi ko kuma abin da suke wato aikin da suke yi abin da ake biyansu bai taka kara ya karya ba don haka halin zaman gida da ake ciki ya Sanya su dole suna bukatar taimako, ga shi kuma mun fara aiwatar wa a kamar yadda kowa zai iya gani”.
Abba Anas, ya ci gaba da cewa suna saran nan gaba kadan za a yi abin da ya fi wannan da aka gani, saboda muna saran samun abin da ya fi haka a nan gaba daga wuraren da muka rubuta masu takardun neman a tallafa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.