Makarantar Islamiyya ta Madrasatu Haqqil Mubeen dake garin Dangoma a Karamar Hukumar Jama’a ta jihar Kaduna ta yaye xalibai 31 da su kayi saukan karatun Qur’ani; mata 29, maza 2 tare da kaddamar da neman taimakon karin ginin azuzuwa a makarantar.
Yayinda yake jawabi a wajen bikin saukan karatun, wanda ya assasa makarantar, Mallam Hamza Ibrahim Na-kawu, ya bayyana takaicinsa kan yadda samari ke baya-baya wajen koyon ilmin addini a yankin, yayinda mata kan yi wa musu zarra, inda yayi kira ga manya da yara da su tashi tsaye wajen neman ilmin addini don samun linzamin gudanar da kyakkyawar rayuwa.
Sannan ya jawo hankalin wadanda su kayi saukan da su kara zage damtse don ci gaba da koyon sauran fanni na addini tare da dabbaka abinda suka karanta a aikace.
Shugaban Hukumar Gudanarwa ta makarantar, Alhaji Ayuba Adamu Musa yace an kafa makarantar ce shekaru 19 da suka wuce da azuzuwa biyu don haka ne suke neman karin wasu azuzuwan saboda makarantar a yanzu tana da dalibai fiye da 500.
“Don haka muke kara yin kira ga iyayen yara da masu hannu da shuni da su taimaka wajen karin azuzuwa a makarantar don amfanin ‘ya’yan musulmai dake yankin.” Inji shi
Shi kuwa Mallam Audi Idris Audi, wanda shine babban bako mai jawabi a wajen, yayi bayani ne kan falala da muhimmancin koyo da kyautata karatun Qur’ani ga mutum tun yana karami domin samun sauki idan ya girma, “domin ilmin yaro qarami kamar zane ne a kan dutse.”
Yace wajibi ne ga mai neman ilmin Kur’ani da ya koyi ilmin Tajwidi don karanta shi yadda ya kamata tare da kaucewa kurakurai.
A karshe an ba daliban takardar shahadar saukan karatun bayan sun gama karatu daga Al-Qur’ani mai girma.
Daga cikin wadanda suka halarci taron saukar akwai Kuyambanan Kaninkon Alhaji Alhassan da Wamban Kaninkon kuma tsohon Hakimin Dangoma, Alhaji Mahmuda Sulaiman da Galadiman Dangoma, inda babban mai kaddamarwa, Alhaji Muhammad Umar ya bude da naira dubu 20 sannan mai bi masa, Alhaji Bashir ya ba da naira dubu 15 kafin sauran jama’a suka ci gaba da hada gudummawarsu.