Home / Big News / Marigayi Shaikh Dahiru Bauchi Ginshikin Zaman Lafiya Da hadin Kan Kasa Ne – Gbenga Hashim

Marigayi Shaikh Dahiru Bauchi Ginshikin Zaman Lafiya Da hadin Kan Kasa Ne – Gbenga Hashim

Daga Imrana Abdullahi
Gbenga Olawepo Hashim, da ya yi takarar Neman kujerar shugabancin Najeriya ya bayyana marigayi Shaikh Dahiru Usman Bauchi da cewa wani muhimmin mutum ne da ya dade ya na kokarin tabbatar da zaman lafiya da kuma Hadin Kan Kasa Baki daya.
A cikin wata takardar da ya Mika gaisuwa ta’aziyyarsa, Hashim ya bayyana shahararren malamin addinin Musulunci a matsayin mutum Mai dimbin ilimi da ya dade ya na kokarin aikin hadin Kan Kasa da ya Jima tsawon lokaci a fannin bautar Allah da taimakawa bil’Adama.
Hashim ya ce hakika marigayi Shaikh Dahiru Bauchi ya Fadakar tare da ilmantar da dimbin al’umma miliyoyi a Kan addinin Musulunci a Najeriya har ma da kasashen waje.
Ya kuma bayyana cewa irin kokarin da marigayin ya yi wajen karantarwa da kokarin saita al’umma ta hanyar tarbiyya da shugabanci duk sun yi WA kasa da al’ummarta amfani musamman a lokacin da aka Shiga cikin wani mawuyacin halin na kalubalen.
 Kamar yadda Hashim, ya bayyana marigayin ya kasance sanannen malamin addinin Musulunci da ya shahara wajen batun Samar da zaman lafiya, taimakekeniya a tsakanin Juna da samun Yan uwa taka da makyabtaka Mai kyau duk da nufin kawar da matsalar samun rarraba a tsakanin Juna.
“Marigayi Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya kuma koyawa dimbin Jama’a yadda za su zauna lafiya musamman ma mabiyansa Wanda Sakamakon hakan ya Samar da wani kyakkyawan Ginshikin Hadin Kan Kasa inda ayyukansa suka Zama abin KO yi”.
Hashim, ya kuma karfafa WA Yan Najeriya da cewa su yi hakuri duk da sun yi rashin Wanda ya wuce kawaii shugaban addini domin wata murya ce da Jama’a ke son ji musamman a lokacin da aka Shiga cikin wani mawuyacin hali da nufin samawa Jama’a mafita ta hanyar Zaman Lafiya a zamantakewa..
Hashim ya kuma Mika gaisuwar ta’aziyyarsa GA iyalai, Yan uwa da abokan arzikin marigayin Shaikh Dahiru Usman Bauchi inda ya yi Kira a gare du da su ci gaba daga wurin da marigayin ya tsaya na yada ilimi da kuma tabbatar da kyakkyawar tarbiyya a cikin al’umma.
Hashim ya kuma Mika ta’aziyyarsa tare da tausayawa jama’ar Jihar Bauchi inda ya ce lallai rashin wani Babban al’amarin ne ga Jihar da kuma kasa Baki daya. Sai ya shawarci Gwannatin jihar ta ci gaba da yin riko da kuma aiwatar da Halayyar marigayin wajen Fadakar wa a Kan amfanin Zaman Lafiya kamar yadda marigayin ya yi aikin ginawa a tsawon lokacin rayuwarsa.
Ya kuma Mika sakonsa GA al’ummar darikar Tijjaniyya a duniya Baki daya inda ya bayyana rashin a matsayin wani Abu Mai ta BA zuciya, sai ya yi Kira GA dimbin mabiyan da su ci gaba da Zama a dunkule wurin daya domin yin riko da karantarwar shugaban marigayi Shaikh Dahiru Usman Bauchi.
Sai ya karfafawa Yan Siyasa da shugabannin addini a fadin kasa Baki daya da su yi koyi tare da dorawa daga inda Shaikh Dahiru Bauchi ya Bari ta yadda za a ci gaba da Gina kasa da jama’ar Baki daya.
 Hashim ya kuma kammala tare da yin addu’ar Neman gafarta  GA marigayin da kuma BA Musulmi hakurin jure rashin da aka yi. Ya kuma ce ya na da karfin gwaiwar cewa nasarori da ayyukan da marigayin ya Bari za su ci gaba da yin jagora wajen Samar da zaman lafiya da hadin Kan Kasa a ci gaba da samun Zaman Lafiya da hadin Kan al’umma Baki daya ta yadda hakan zai amfanar da wadansu al’ummu masu zuwa nan gaba.

About andiya

Check Also

SHUGABA KARAMAR HUKUMAR FUNTUA YA YABA WA GWAMNA RADDA KAN KIRKIRAR CIBIYAR KOYON SANA’O’I A FUNTUA

  Shugaban Karamar Hukumar Funtua, Alhaji Abdulmutallab Jibrin Sulaiman Goya, ya bayyana jin daɗinsa tare …

Leave a Reply

Your email address will not be published.