Daga Imrana Abdullahi
Alhaji Kabiru Yunusa, ya bayyana ranar babban taron da dan uwansa dan majalisar Jiha mai wakiltar mazabar Unguwar Sanusi Auwalu Yahaya da ake yi wa lakabi da Yaro mai kyau da cewa rana ce ta yin farin ciki , murna da kuma yin hamdala ga Allah madaukakin Sarki.
Kabiru Yunusa ya ce dole ne ayi wa Allah godiya da farin ciki domin rana ce da ake taimakawa wadanda ba su da shi ta fuskar yin karatu da sauran wadansu fannoni na rayuwar bil’adama.
Alhaji Kabiru Yunusa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a wajen taron da aka yi a babban dakin taro na makarantar Sakandare ta Ahmadu Cancangi da ke Kaduna.
Yunusa ya ci gaba da cewa, ” abu ne da ke gagarar wadansu iyaye da ba su da shi, amma shi ya bugi kirji yake biyawa yara yan makaranta domin su rubuta jarabawar fita makarantar Sakandare,da ainihin kudin ke kamawa daga dubu Hamsin har Sttin amma ya cire ya biyawa dalibai masu yawa haka da suka kai 120 koma sama da haka kuma ya na aiwatar da wannan kokarin na tsawon shekaru da suka gabata ya na taimakon yaran da iyayensu ba za su iya daukar nauyin su ba don haka muna yi wa Allah godiya da Allah ya kawo mi wannan lokacin”.
” shi kuma muna yin masa addu’a Allah ya kara masa karfin arziki, juriyar da zai taimaki al’umma”, inji Kabiru Yunusa.
A game da yaran da suka amfana kuma Alhaji Kabiru Yunusa ya kara da cewa ya na yi masu fatan alkairi da kuma yin kira a gare su da su ba marada kunya kowa ya yi kokari a kai su sharewa iyayensu hawaye kuma shima su kara mashi karfin Gwiwa ya kara yin hobbasa a kan abin da yake yi ya ga ya taimakawa mutane a samu al’umma tagari da kowa zai yi alfahari da ita. Muna yi masu fatan alkairi su dauki zuciyar taimakawa al’umma idan mutum ya kai matsayin da zai taimaka.
“A matsayina na wanda keda ilimin yin hulda da jama’a da ya shiga kusan kowa ne bangare na kasa tun daga bangaren yankin Yarbawa da kasar Igbo da yankin Kudu masu Kudu duk ba inda ban zauna ba, hakika na ga yankin Arewa an bar mu a baya saboda ko a yanzu abin da ke kara kai mu baya shi ne batun matsalar tsaron nan da rashin ilimi ya na daya daga ciki domin a duk inda kaga an ci gaba ai duk batun ilimi ne babu abin da za a hada shi da ilimi domin shike wayar da kan al’umma ya kuma nuna maka abin da ya dace ka yi har ma ka san mutane ka san maga ba da kai ka rika rarrabe wa a tsakanin al’umma kowa ka ba shi hakkin sa