Home / Labarai / Muna Son A Lalubo Hanyoyin Warware Matsalar Tsaro A Najeriya – Sada Soli

Muna Son A Lalubo Hanyoyin Warware Matsalar Tsaro A Najeriya – Sada Soli

Bashir Bello Majalisar Abuja
Honarabul Sada Soli dan majalisar wakilai ta tarayya ne mai wakiltar kananan hukumomin Jibiya da Kaita a Jihar Katsina ya bayyana cewa suna son a lalubo hanyoyin warware batun matsalar tsaron da ke addabar yankin Arewa maso Yamma a tarayyar Najeriya sakamakon irin yadda ake yin Kwan gaba Kwan baya a game da lamarin.
Sada Soli ya ci gaba da bayanin cewa suna bukatar a zauna domin a san me ya dace ayi ta yadda za a daina satar jama’a ana karbar kudin fansa daga jama’a suna ta yin asarar kayansu da dukiyarsu ba gaira ba dalili.
” Idan sasanci za a yi to, da wa za a yi shi kuma ta yaya za a yi sasancin duk wadannan abubuwan ya dace a duba wadannan ba a rika ganin laifin shugabannin mu ba , ba ma kamar Jagororin domin idan ka ji irin kudin da ake kashewa a matakin jiha a kan batun matsalar tsaron da ake fama da shi musamman irin kudin da ake kashewa jami’an tsaro don haka idan za a yi fada da mutanen nan a zauna ayi shawara da su domin a daina ganin laifin su “.
Dan majalisa Sada Soli ya kara da cewa tsayar da ta’addanci na da hanyoyi da yawa don haka idan wannan hanyar ta toshe sai a dubi wata kuma da ban saboda haka ba wai mutum daya ba ne keda basirar tsayar da duk wani abu ta’addanci dole sai an kawo hanyoyi da shawarwari da tunanin jama’a da dama, musamman masu ilimi da masu ruwa da tsaki da wadanda suke da abin nan suke tare da mutanen nan da wadanda suke a cikin al’umma suna tafiyar da al’amuran jama’a a kawo su a cikin tafiyar a zauna da su a nemi mafita ba wai kawai a rika yin taron kaddamar da wani ko wasu shirye shiryen ba da wadanda ba su ma san me mutanen ke ciki ba a rika kaddamar da kaza da kaza haka kawai”.
Ya kuma tabbatar da cewa, “Gwamnoni kansu a hade yake din haka ne ya dace a samu hadin kai tare da mutanen da suke jami’an tsaron da ke jagorantar lamarin nan. Sai dai muna tunanin akwai kazalanda a yadda ake gudanar da lamarin nan domin tuni an ci karfinsa”.
“Sakamakon hakan ne majalisa ta yi kudiri a kan a jawo hankalin shugaban kasa a san hanyoyin da za a bi na tsare tsare a kawo karshen lamarin baki daya. Jami’an tsaron da Jihohin Katsina da Zamfara suka kirkiro suna da amfani kwarai domin mutane ne da suke da kishin al’ummarsu don sun san lunguna da sako na garuruwansu kuma suna taimakon jami’an tsaron nan suna  tafiyar da ayyukansu.
“Kalamin majalisa a kan wannan lamari zai yi tasiri kwarai kasancewar furucin majalisa furuci ne mai tasiri wajen tafiyar da al’amuran Gwamnati
“Don haka ne majalisa ta bukaci shugaban kasa da ya kira shugabannin tsaron nan ya kuma yi masu magana da su kara kaimi a kawo karshen matsalolin tsaron nan kuma su hada kai da Gwamnatocin jihihi ta yadda kwalliya za ta ci gaba da biyan kudin sabulu”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.