Tsohon Gwamnan Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce ya samu gayyata ta musamman daga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya zuwa birnin Amurka “New York” na kasar Amurka.
Malam Shekarau ya ce ba a yi masa cikakken bayani ba kan dalilin gayyatar da aka yi masa ba, amma mako mai zuwa zai amsa gayyatar.
A wani sako da Jibril Muhammad Na-Tara, mai taimaka wa tsohon gwamnan kan kafafen sada zumunta da daukar hoto ya wallafa, ya tabbatar da gayyatar da ya aike wa tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau.
Tun da aka fara yada cewa Majalisar Dinkin Duniya za ta baiwa tsohon Gwamnan Kano mukami, Malam Ibrahim Shekarau ya ce babban sakataren ya gayyace shi, kuma shi kansa bai da cikakken bayanin dalilin gayyatar da kungiyar ta yi masa. Majalisar Dinkin Duniya.