Home / Big News / Rashin Shugabanci Nagari Ne Matsalar NaJeriya – Farfesa Kailani Muhammad

Rashin Shugabanci Nagari Ne Matsalar NaJeriya – Farfesa Kailani Muhammad

Daga Imrana Abdullahi

Farfesa Kailani Muhammad ya bayyana cewa shugabannin Najeriya a halin yanzu duniya kawai suka tasa a gaba sabanin irin shugabannin can baya da suke tunanin Lahirarsu.

Farfesa Kailani Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a kan batun cikar Najeriya shekaru  sama da sittin.

Farfesa Kailani Muhammad ya ce su wadancan shugabanni sun rike gaskiya da amana ne domin samun tsira a ranar gobe kiyama, amma na yanzu kyalkyalin duniya kawai don in ba haka ba mutum ya dace ya tuna da ranar da zai mutu kuma ya tuna cewa wanda ya fi kowa a cikin ku shi ne wanda ya fi tsoron Allah ba tarin dukiya ba sai dai me mutum yazo da shi na alkairi kawai.

” Sai kaga mutum bayan ya yi minista sai ya koma Gwamna daga nan sai mutum ya shiga majalisar dokoki ta kasa kuma ba abin da yake tsinanawa Allah ya saukake.

” 2027 ta doso kuma mu muka kawo gwamnatin nan in ba mun gyara ba sai dai muce lahaula wala kuwata illa billah domin abin zai fi haka, kuma babu alamun gyara ya zuwa yanzu kuma wani abu da shugaban kasa ke yi wa kasa jawabi shi ne ya na cewa ya na ba gwamnoni kudi tiriliyoyi domin kudin yaje ga talaka har sau hudu ya na fadin hakan amma kai ka gani, in da za su yi domin Allah talaucin nan ya yi yawa da ba za a gani ba duk mai yin yaudara kansa yake yaudara ba talakawa ba domin Allah ya na kallo, me zai hana a duk arewacin Najeriya inda duk Islamiyya take a kawo darussan ilimin boko a wajen a rika karantarwa don haka hakkinmu ya na kandu kuma sai Allah ya kama su da shi.

“Sai da aka kai karan mu a wajen shugaban kasa domin

 kawai munce za mu yi aiki da zai kai Sanata Yari shugaban majalisar dattawa domin kawai shi Dan arewa ne zai rika duba al’amura sosai idan kuma za a jima mutanen arewa zai ce a’a ya zama garkuwa gare mu. Tun da aka cure tallafin mai aka kuma yi maganar Dola na kudi sai aka ba ta komai ga kuma yawan haraje haraje da ya yi yawa tun daga kudin Banki, NEPA har yanzu ma akwai wani kashi biyar da aka ce za a sanya na tashin Jirgi ko ina dai haraji haraji kawai”.

Har ma na ji Lauya Frmi Falana ya fito ya ce tiriliyoyin da ake samu na tallafin mai ina ake kai su sai ciyo bashi bashi kaaai ake ta yi, tun da nake tare da marigayi Muhammadu Buhari a shekarar 2002 ban ta ba can za sheka zuwa wani wuri ba domin muna da akida na azo a gyara kasarmu kowa ya samu walwala yakamata mutane suji tsoron Allah shugabanni su tashi tsaye ayi gyaran da zaa zauna lafiya amma ace duk dukiyar da muke da ita wani Dan Najeriya ba shi da abin da zai ci ai dole sai Allah ya tambaya

About andiya

Check Also

Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861 Ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 …

Leave a Reply

Your email address will not be published.