Home / Labarai / Sai Mun Ga Bayan Ta’addanci A Jihar Zamfara – Matawalle

Sai Mun Ga Bayan Ta’addanci A Jihar Zamfara – Matawalle

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Dokta Muhammad Bello Matawallen Maradun ya bayyana cewa ya na nan a cikin Jihar Zamfara tare da sauran al’umma a kokarin ganin an magance aikin yan Ta’adda da ayyukansu baki daya don haka kowa ya kara hakuri aikin da ake yi nasara ce ga kowa da kasar baki daya.
Gwamnan ya dai bayyana hakan ne a lokacin da ya dawo zagayen ganewa idanunsa irin yadda lamarin maganin yan ta’addan le faruwa a sansanoninsu da suka a cikin Daji.
“Ina nan cikin Zamfara ba inda zan je, sai mun kammala kai ma yan banza farmaki, mun karya musu logon karfinsu, mun lallata musu kayan aiki. Manufar mu shine mu magance barazana tsaro da suke yiwa al’ummar mu. Zan ji yadda kowa yake ji a Zamfara, zan dandani kowane iri yanayi tare da mutane na don ganin goben mu tafi yau dadi da kyau saboda makoma ga al’umma baki daya….”
Gwamnan #Bello_Muhammad Mutawalle ga al’umma jahar Zamfara a jiya bayan dawowa daga duba wurare da Sojoji ke kai farmaki.
– Ibrahim Yusuf Dan Hausa

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.