Related Articles
Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamna Mai Mala Buni na Yobe, a ranar Litinin ya yi kira ga bankunan kasuwanci da su kara kafa rassa a fadin jihar domin saukaka hada-hadar kasuwanci.
Buni ya yi wannan roko ne a Damaturu a lokacin da yake kaddamar da injuna 50 cire kudade da turawa Point Of Sale (POS) da bankin United Bank for Africa (UBA) ya baiwa jihar domin bunkasa kudaden shiga.
Ya ce kara kafa wasu rassa a fadin jihar zai karfafa hada-hadar banki a tsakanin mazauna karkara matukar gaske.
“A cewar Gwamnan a duk fadin Jihar Yobe, kananan hukumomin da ke da bankuna an da suke aiki ba su wuce hudu ba daga cikin kananan hukumomi 17 ke da bankuna. Yawancin mutanenmu ko dai manoma ne ko kuma makiyaya da suka yi imani da rike tsabar kudi maimakon hada-hadar banki.
“Lokaci ya yi da za ku fadada ayyukanku don bude Rassan ku a sauran kananan hukumomin,” in ji gwamnan.
Buni ya lura da a cewa matukar bankunan suna da rassa da yawa, labudda canza tsoffin kudaden daidai da manufar sake fasalin Naira na Babban Bankin Babban Bankin zai yi nasara.
“Don haka Ina kira ga bankunan da su kara wayar da kan jama’a game da manufofin tare da samar da hanyar da mutane za su iya canza tsoffin takardun su zuwa sabo cikin sauƙi kafin ranar 31 ga Janairu, 2023, ranar ƙarshe,” in ji shi.
Gwamnan ya yabawa bankin UBA bisa wannan tallafin wanda a cewarsa hakan zai saukaka wajen samun kudaden shiga da kuma tara kudaden shiga.
Buni ya yabawa bankunan kasuwanci da sauran abokan ci gaban kasa bisa goyon bayan jihar wajen aiwatar da manufofi da shirye-shirye masu tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma.
A nasa jawabin, shugaban hukumar tara kudaden shiga na cikin gida, Alhaji Abatcha Geidam, ya bada tabbacin yin amfani da injinan yadda ya kamata.