Daga Imrana Abdullahi
Sanata mai wakiltar Kaduna ta Kudu Sanata kuma wanda ya kafa gidauniyar Marshall Katung Foundation (MKF), Sunday Marshall Katung ya amince da fara shirin bayar da tallafin karatu na karo na biyu na gidauniyar ga dalibai marasa galihu na manyan makarantu daga gundumar sa ta majalisar dattawa da ke yankin Kudancin Kaduna.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da Sa hannu
Umar Bin Sakataren gudanarwa.
Ɗaya daga cikin mahimman manufofin gidauniyar ita ce ƙarfafawa da tallafa wa ɗaliban da ba su da kuɗi don neman ilimi mafi girma ta hanyar tallafin karatu.
Har ila yau, irin wannan kokarin nasa na bayar da tallafin maido da fata a tsakanin daliban da ke daf da barin karatu, saboda rashin iya biyan kudin karatunsu, sakamakon matsalolin tattalin arziki da na kudi da rayuwar jama’a ke fuskanta.
An yi la’akari da hikimar karin maganar Sinawa da ke cewa, idan kuna shirin shekara guda, ku shuka shinkafa; idan kuna shirin shekaru Goma, dasa bishiyoyi; idan kuna shirin rayuwa har abada, ku ilimantar da mutane, wannan hangen nesa ne ya zaburar da dan majalisar domin tallafawa karatun dalibai a Kudancin Kaduna don kare gaba da samar da ci gaba mai dorewa.
Yunkurin ya dade yana ci gaba kuma ya hada da tallafin ilimi a kananan hukumomi ta hanyar ginawa da gyara makarantu da cibiyoyin sana’a; Shirye-shiryen Fom na yin jarabawar shiga jami’a wato, “JAMB”, kyauta; samar da littattafai da kwamfutoci zuwa makarantun sakandare, tsare-tsaren tallafin karatu, da dai sauransu.
Gidauniyar tana da niyyar sanya ilimi ba kawai abin sha’awa ba ne har ma da arha ga duk yaranmu masu son yin karatun
A cikin wannan sabon rukunin guraben karo karatu, ƙwararrun ɗalibai maza da mata za su zaɓi waɗanda suka cancanci samun digiri nagari waɗanda suka haɗa da Malamai, lauyoyi, ƙungiyoyin jama’a, ‘yan jarida da shugabannin ƙungiyoyin al’umma.
Don haka, Gidauniyar Marshall Katung tana gayyatar dalibai masu sha’awar karatun digiri na farko daga kananan hukumomi takwas (8) na gundumar Kaduna ta Kudu da ke karatu a manyan makarantun gwamnati a Najeriya don neman tallafin karatu na bana.
Saboda haka ne ake shaidawa jama’a cewa an buɗe daga Juma’a 25 ga Agusta, 2023 kuma a rufe tsakar daren Alhamis 31 ga Agusta 2023.
HANYAR APPLICATION
Masu bukata su shiga: https://formfacade.com/sm/lDovLicyK
24/08/2023