Home / Labarai / SANATA UBA SANI YA YI TIR DA KISAN MUTANE 19 A BIRNIN GWARI DA KAJURU

SANATA UBA SANI YA YI TIR DA KISAN MUTANE 19 A BIRNIN GWARI DA KAJURU

SANATA UBA SANI YA YI TIR DA KISAN MUTANE 19 A BIRNIN GWARI DA KAJURU

 

Nasiru DanBatta

 

 

Sanatan da ke wakiltar Kaduna Ta tsakiya a Majalisar Dattawan Nijeriya Sanata Uba Sani ya yi tir da harin da ‘yan bindiga suka kai kauyukan Kananan hukumomin Birnin Gwari da Kajuru.

 

Sanatan ya bayyana rashin jin dadinsa bisa wannan hari yana mai mika ta’aziyyarsa ga ‘yan uwan wadanda aka rasa a wannan harin.

 

sannan kuma ya yi kira gwamnati na ganin an kawo karshen hare-haren kauyuka a yankin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

 

Bayan haka ya jinjinawa gwamnatin Jihar Kaduna karkashin gwamna Malam  Nasir  Ahmad El-Rufai kan kokarin da take yi wajen ganin an kawo Karshen hare-haren ‘yan bindiga a jihar.

 

Sanatan ya kara da cewa za a aika da kayan tallafi na gaggawa ga wadanda wannan ibtila’i ya afka wa yana mai kira ga mutane da su kwantar da hankulan su.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.