Shugaban matasa na jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso Yamma Alhaji Atiku Muhammad Yabo, ya bayyana abubuwan da dan majalisar wakilai na tarayya da ke wakiltar karamar hukumar Igabi Honarabul Husaini Muhammad Jalo keyi a matsayin abin a yaba tare da Jinjinar bangirma.
Atiku Muhammad Yabo, ya ce hakika su a matsayinsu na shugabannin jam’iyya suna yabawa da irin yadda Honarabul Husaini Muhammad Jalo na koyawa yara sana’o’i da Koyar da Noman zamani da cewa hanya ce ta samun ci gaban al’umma.
Atiku Yabo, ya ci gaba da cewa irin abubuwan da muke gani Honarabul Jalo na yi abin murna ne da farin ciki ga duk dan jam’iyyar PDP da masu son ci gaban kasa tare da al’ummarta, sabina a samu dan majalisar wakilai ya na mayar da hankalinsa a fannonin ayyukan sana’o’i da aikin Gona kuma ya bayar da kayan Noma da suka hada da Injunan banruwa da sauran muhimman kayan Noma kuma ga irin yadda dan majalisar ke raba wa jama’a Baburan hawa da jama’a ga kuma koyawa al’umma sana’o’in da za su dogara da kansu.
“Ya koyawa mata da matsa a karamar hukumar Igabi a kalla mutane dubu daya da dari biyar sana’o’i daban daban 1,500 ga kuma rabon Kekunan dinki, injunan Banruwa sai kuma kudi naira dubu dari ga kungiyoyi da dai kyautar kudi ga jama’a da dama a karamar hukumar Igabi domin a samu ci gaban da kowa ke bukata
Atiku Yabo ya ce game da ayyukan samar da kyakkyawan wakilcin da wannan dan majalisar ke yi a kullum ya na faranta mana zuciya kwarai.
Hakika muna goyon baya da yin kira ga daukacin wadanda aka zaba karkashin tutar jam’iyya PDP da su yi koyi da irin ayyukan alkairi da kuma kokarin raya al’ummar da Honarabul husaini Muhammad Jalo ke yi da nufin kara habbaka harkokin Dimokuradiyya da siyasa baki daya.