Home / Big News / Taimakon Talakawa: An Yaba Wa Gwamna Yobe Mai Mala Buni 

Taimakon Talakawa: An Yaba Wa Gwamna Yobe Mai Mala Buni 

Daga Imrana Abdullahi
Shugaban karamar hukumar Bade a Jihar Yobe, Ibrahim Babagana ya bayyana jihar Yobe karkashin jagorancin Mai Mala Buni da cewa ita ce kan gaba wajen harkar kulawa da manoma a duk fadin Najeriya.
Ibrahim Babagana ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala babban taron ranar Jihar Yobe da aka yi a bikin kasuwar duniyar kasa da kasa a Kaduna.
Babagana ya ci gaba da bayanin cewa hakika a Jihar Yobe an yi sa’ar jajirtaccen Gwamna mai son jama’a tare da ƙoƙarin inganta rayuwarsu a fannoni daban daban.
“Da an ambaci karamar hukumar Bade za a GA cewa wuri ne da yake a kan Ruwa don haka jama’arta sun shahara a batun Noma musamman na Shinkafa,Alkama da Noman abin da ya shafi Danyen kaya, sannan kuma a karamar hukumar Bade ana yin Noman Kifi kamar yadda kuke gani a yanzu akwai manya manyan Kifayen da aka zo da su daga can karamar hukumar Bade zuwa wannan kasuwar domin nunawa duniya irin hobbasar da ake yi a karamar hukumar,Kuma shi wannan Kifin da muka zo da shi a cikin Kogi ake samunsa duk girmansa kamar yadda ake gani.
Ya kara da cewa a karamar hukumar za a samu abubuwan da suke na gargajiya da yawa wanda ba alfahari ba idan aka duba kananan hukumomi da yawa ba su da abin da muka zo da shi saboda mu a zahirin gaskiya abin da muke da shi ne muka zo da shi a nan kasuwar Duniya ta kasa da kasa da ke Kaduna.
“Kasancewar karamar hukumar Bade mai zaman lafiya da kwanciyar hankali wanda a kullum muke kokarin fadakar da duk wani mai son zuba hannun Jari da ya zo ya zuba jari a ɓangarorin ci gaban tattalin arziki daban daban, kasancewar Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni na kokari kwarai wajen samun tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin jama’a. Karamar hukumar Bade na da wadataccen Ruwa da isasshen filin da duk abin da mutum ke son ya Noma zai Noma akwai kwararrun mutanen da suka san aikin da duk abin da mutum ke son ya samu zai samu domin akwai wadanda suka san aikin, sannan kuma akwai wadataccen ingantaccen iri karamar hukumar Bade don haka ne muke yin kira ga duk masu zuba hannun jari da su zo jihar Yobe kuma a karamar hukumar Bade domin biyan buƙatar zuba karin da suke don yi.
“Mu tsakanin mu da Gwamnan Yobe Mai Mala Buni sai dai mu ce masa Allah ya saka masa da alkairi domin tun da jihar Yobe take ba a ta ba samun wanda ya taimakawa jama’a Talakawa ba kamar Alhaji Mai Mala Buni ba domin ya taimakawa da Talakawan da ba su ta ba tsammani ba da kayan Noma,Taraktocin Noma masu saukin aiki, ya kuma taimakawa Talakawa da Takin zamani ga kuma taimakon kudi da za su yi amfani da shi a Gonakansu, sannan kuma ya sa an taimakawa kowa ne manomi da ruwan da zai kai har Gonarsa domin ayi amfani da shi wajen Noma don haka idan zamu lissafa wa duniya irin abubuwan da Alhaji Mai Mala Buni ya yi wa Talakawan Yobe ba dai a cikin karamin lokaci ba don haka sai dai muce Allah ya saka masa da alkairi kawai.

About andiya

Check Also

Gwamna Lawal Ya Lashe Kyautar Gwarzon Gwamnan Shekara Ta Jaridar LEADERSHIP, Ya Sake Jaddada Ƙudirin Ci Gaban Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake tabbatar da ƙudirin gwamnatin sa na kawo …

Leave a Reply

Your email address will not be published.