Home / Labarai / TINUBU YA SAUKA DAGA KAN KUJERAR SHUGABANCIN KUNGIYAR ECOWAS – FARFESA ABDULLAHI

TINUBU YA SAUKA DAGA KAN KUJERAR SHUGABANCIN KUNGIYAR ECOWAS – FARFESA ABDULLAHI

Daga Imrana Abdullahi

Farfesa Abdullahi Mustapha tsohon mataimakin shugaban jami’ar Ahmadu Bello ne da ke Zariya kira ya yi ga shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya sauka daga kan kujerar shugabancin kungiyar ECOWAS idan har aka matsa masa sai an kai wa kasar Nijar hari.

Farfesa Abdullahi Mustapha ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron Lacca da aka yi a masallacin ITN da ke Zariya.

Farfesa Abdullahi Mustapha ya ce hakika mu ba mu goyi bayan kaiwa kasar Nijar hari ba don haka idan har shi shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ga an matsa masa lamba sai ya kai wa Nijar hari to, ya sauka daga shugabancin kungiyar ECOWAS ya tsaya a matsayin shugaban mu na Najeriya kawai.

Ya ci gaba da bayanin cewa ” su ne suka shirya wannan taron Laccar domin a fadakar da yan uwa irin illar da ke tattare da kai wa yan uwan mu yan Nijar hari don haka maganar ma ba ta ko taso ba, saboda ga duk wani mai fikira ta sanin tarihi ya san babu wani abin da za a ce zai hada mu fada tsakanin mu da Nijar wannan ne ya sa muke fadakar da mutane kuma su shugabannin da muka zaba. Wato kuma shi shugaban kasa na Najeriya da aka zaba ya san cewa kuri’ar Arewa ce ta kawo shi kan karagar mulki, don haka an zabe shi ne yazo ya gyara Najeriya fituntunun da muke da su na Boko haram da kashe karshen mutane a magance su ya gyara kasa don ba ECOWAS ba ce ta zabe shi ba saboda haka idan har wannan hular da aka bashi na shugabancin ECOWAS muna bashi shawarar ya cire ta ya ba su abin su ya dawo ya zama shugaban kasa na Najeriya ya yi aikin da aka zabe shi domin sa kawai”.

Kuma muna kiran yan uwa yan Najeriya da su tashi tsaye mu nuna lallai ba mu yarda ba a game da abin da ake son yi.

” Ita kuma Faransa da Amerika su Sani duk da karfin da suke da shi mun kai kukan mu ga Allah madaukakin Sarki da duk abin da ya so haka zai kasance, Kahirujabbar da zai yi maganin duk wani shakiyyi a ko’ ina yake”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.