Daga Imrana Abdullahi
Bayanin da muke samu na cewa tsohon shugaban majalisar wakilai ta Takwas (8) Alhaji Ghali Umar Na’ABBA ya rasu.
Tsohon shugaban majalisar wakilan dai an haife shi ne a ranar 27 ga watan Satumba, 1958, an kuma san shi da tsayawa a kan kokarin kare muradun yankasa a koda yaushe.
Ya dai rasu ne da sanyin safiyar ranar Laraba 27 ga watan Disamba, 2023.
Marigayin dai ya zamo shugaban majalisar wakilai ne a shekara ta dubu biyu (2000) bayan da aka matsawa tsohon shugaban majalisar Salisu Buhari yin Murabus, duk a sakamakon wata matsalar shaidar karatu daga makarantar jami’ar Toronto.
Marigayi tsohon kakakin majalisar wakilan Ghali Umar Na’ABBA dai ya wakilci mazabar karamar hukumar cikin birnin Kano ne a Jihar Kano arewacin tarayyar Najeriya.