Related Articles
Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 13, Sun Ji Wa 7 Rauni A Zangon Kataf, Kauru Da Chikun
Mustapha Imrana Abdullahi
….Gidaje 56, Babura 16 aka Kona A karamar hukumar Kauru
Bayanai da suke fitowa daga Jihar Kaduna na cewa an halaka mutane 13 wadansu Bakwai sun samu raunuka sakamakon wadansu hare haren da aka kai wa wadansu mutane a kananan hukumomin Zangon Kataf, Kauru da Chikun duk a Jihar kadina.
Wannan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa mai dauke da sa hannun Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Malam Samuel Aruwan da aka rabawa manema labarai a Kaduna.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta samu wannan rahoton ne daga jami’an rundunar Sojan Nijeriya karkashin rundunar ( Operation Safe Haven) da ke aikin tabbatar da tsaro a wannan yankin.
Kamar yadda rahoton ya bayyana wadansu yan bindiga masu dauke da makamai sun kaiwa wani mutum mai suna Irmiya Godwin hari tare da dan uwansa lokacin da suke dawowa daga Gona a kauyen Gora Gan a cikin karamar hukumar Zangon Kataf. Nan da nan aka kashe Irmiya Godwin, dan uwansa kuma ya tsira.
A wani bayanin rahoton kuma wasu yan bindiga sun kai hari a kauyen Kizachi a karamar hukumar Kauru, sun kuma kashe mutane 10 inda suka bar wadansu guda hudu da raunuka. An kuma Kone gidaje 56 da Babura 16 duk sun ci wuta da sauransu.
Wadanda aka kashe sun hada da:
– Esther Bulus
– Maria Bulus (one-year-old daughter of Esther)
– Lami Bulus
– Aliyu Bulus
– Monday Joseph
– Geje Abuba
– Wakili Filibus
– Yakubu Ali.
– Dije Waziri
– Joseph Ibrahim
Wadanda suka samu raunuka sun hada da:
– Cecilia Aku
– Yakubu Idi
– Godiya Saleh
– Moses Adamu.
Wadanda suka samu raunukan suna can a asibiti ana duba lafiyarsu.
A ci gaba da rahotan Gwamnatin a wani kauye kuma mai suna Masaka a karamar hukumar Chikun an kai masu hari. Inda aka kashe wani mai suna Duza Bamaiyi, an kuma ji wa wadansu mutane biyu raunuka. Nan da nan jami’an tsaro suka Isa wurin domin tabbatar da tsaro.
Jami’an tsaron sun bayar da rahoton cewa yan bindiga sun kashe wani mai suna Zakka Pada a Kurmin Kaduna duk a karamar hukumar Chikun, wani mai suna Pada Dalle ya raunata.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i ya bayyana bacin ransa da samun wannan rahoton, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya ya kuma ba iyalansu hakurin jure wannan rashin. Tare da fatan samun sauki ga wadanda suka samu raunuka.