Home / Ilimi / Yan bindiga Sun Sake Kashe Daliban Jami’ar Greenfield Biyu

Yan bindiga Sun Sake Kashe Daliban Jami’ar Greenfield Biyu

Yan bindiga Sun Sake Kashe Daliban Jami’ar Greenfield Biyu
Mustapha Imrana Abdullahi
A wani labari mai abin ban takaici, da jami’an tsaro suka shaidawa Gwamnatin Jihar Kaduna sun ce sun samu gano karin Gawa biyu ta daliban jami’ar Greenfield mai zaman kanta da ke Kaduna a yau ranar Litinin 26 ha watan Afrilu, 2021.
Gawarwakin biyu da aka samu tuni aka kwashe su zuwa wurin ajiyar Gawa na asibiti, kuma an shaidawa mahukuntan jami’ar abin da ya faru.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da ke dauke da sa hannun kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan.
Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagoranci  Malam Nasiru Rl- Rufa’I ta yi bakin ciki kwarai da faruwar wannan lamarin inda aka kashe daliban da suke kokarin neman iliminsu domin gyaran gobe.
Gwamnatin kuma ta aike wa iyalan da abin ya shafa sakon gaisuwar ta’aziyyarta da kuma hukumar jami’ar da addu’ar Allah ya gafarta wa daliban da suka rasu.
Gwamnati ta kuma ce za ta ci gaba da sanar da jama’a abin da ke faruwa a kan lamarin.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.