Related Articles
Bayan dawowarsa daga garin Madina da ke Kasar Saudi Arabiya domin jagorantar jana’izar Marigayi Alhaji Aminu Dantata Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ziyarci iyalan Marigayi Alhaji Aminu Dantata domin yi musu Ta’aziyyar rasuwarsa.
Bayanin hakan na kinshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da Sa hannun
Abubakar Balarabe Kofar Na’isa Sakataren yada labarai na Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR JP CNOL, da aka rabawa manema labarai.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce duniya baki daya ba za ta manta da irin gudunmawar da Alhaji Aminu Alhasan Dantata ya bayar ba wajen ci gaba a fannoni daban daban.
Mai Martaba Sarkin ya jagoranci gabatar da addu’o’i na musamman ga marigayin inda ya yi addu’ar Allah ya jaddada rahama ga Marigayin ya Kuma bawa iyalansa da al’umar jihar Kano da Kasa da duniya baki daya hakurin jure rashinsa.
Kazalika Mai Martaba Sarkin yakan makamanciyar irin wannan ziyarar Ta’aziyyar ga Hajiya Mariya Dantata inda yayi addu’ar Allah ya gafarta masa ba bashi aljanna madaukakiya.
Kamar kowanne lokaci dai Mai Martaba Sarkin ya samu rakiyar Hakimai da sauran al’uma masoya Sarki tun daga fitowarsa zuwa komawa fadarsa dake gidan Nassarawa a birnin Kano.
THESHIELD Garkuwa