Home / Uncategorized / Zannan Bungudu Ya Taimakawa Al’ummar Zamfara Mazauna Kaduna Da Miliyan Goma

Zannan Bungudu Ya Taimakawa Al’ummar Zamfara Mazauna Kaduna Da Miliyan Goma

Muna Kara Yi wa Zannan Bungudu Jinjina kwarai

Daga Imrana Abdullahi

A kokarin ganin al’ummar Jihar Zamfara a ko’ina suke sun zauna da kafarsu kowa ya samu abin yi yasa fitaccen dan siyasa Zannan Bungudu Alhaji Abdulmalik Zubairu, ya bayar da tallafin naira miliyan Goma ga kungiyar Zamfarawa mazaunan Kaduna domin kowa ya tsaya da kafarsa.

Wannan abin alkairi dai ya fito fili ne a wajen kaddamar da bayar da tallafin ga daukacin al’ummar da duka fito daga kananan hukumomi Goma sha hudu (14) da suka fito daga Jihar Zamfara da aka yi a gidan tunawa da marigayi Sardauna wato gidan Arewa a cikin garin Kaduna.

A wajen wannan taron dai Zannan Bungudu ya samu wakilcin mutane har guda uku da suka halarci taron kuma sai da aka raba kudin kaf ga mutane 20 daga kowace karamar hukuma 14 na Jihar Zamafara kuma a gaban jama’a kowa ya fito aka kira sunan sa ya karba da suka hadada maza da mata duk daga jihar Zamfara.

Da yake jawabi ga manema labarai daya daga cikin wakilan Zannan Bungudu Alhaji Abdulkadir Ibrahim Gamji, godiya ya yi ga Allah madaukakin Sarki da al’ummar Jihar Zamfara ta samu nasarar hada kanta wuri guda duk da suna zama a Kaduna da ke da kananan hukumomi 23.

“Duk al’ummar da suka samu kansu a haka sun hada kai da ikon Allah ana tunanin alkairi ne musamman irin wannan shirin da wannan  kungiya ta zo da shi lallai abin a yaba ne kwarai matuka da gaske saboda haka ne muke jinjinawa shugabannin a kan kokarin da suka yi.

Gamji ya ci gaba da cewa ya na yi wa kowa matashiya kamar yadda lamarin ya faru a halin yanzu domin manufar da ta Sanya aka yi wannan kokari na hada kan jama’a ba dadewa ba za ta bayyana saboda da hakan muna saran tattalin arzikin Jihar Zamfara zai Farfado da ikon Allah.

Abdulkadir Gamji ya kara da cewa, ” kamar yadda aka Sani honarabul Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudu, hantsi ne leka gidan kowa ba da dadewa ba ko a ranar 21 ga watan Disamba da ya gabata na 2024, muna Jihar Ondo a masarautar Ekare, yan asalin Jihar Zamfara mazauna Ondo suka ji irin abin da yake yi suka nemi wannan masarautar inda suke zaune su Karrama shi aka bashi sarautar Cif Mayegun of Ekare Oko, wanda an dai ba shi wannan Sarautar tun a watan Satumba da ta gabata amma an nada shi a watan Disamba da ya gabata kuma abin farin ciki ba ma yan Jihar Zamfara ba kawai duk Hausawa mazauna can sun shaida irin rawar da ya taka masu a wurin da irin gudunmawar da ya bayar kai har ma da daga darajar Bahaushe Baki daya”.

Abdulkadir Gamji ya kuma ja hankali ga sauran jama’a na Jihar Zamfara domin kowa ya gane abin da ya dace, ” hakika duk irin kiran da jama’a za su yi ya dace su rika yin kiran abin da yake damuwar mutum don haka duk inda muka samu kan mu yan jihar Zamfara kowa ya san ciwon mu shi ne batun tsaro wanda a yanzu mun shaida irin yadda Jihar Kaduna ta dauki matakin da ya dace aka samu maslaha a kan batun tsaron da ke addabar yankin a can baya har wuraren da a can baya fiye da shekaru Bakwai ba a iya zuwa amma a yanzu komai ya kwaranye ana iya zuwa wurin ba tare da wata matsala ba, wanda hakan ya sa muke fatan Allah ya nuna mana hakan agare mu”, inji Abdulkadir Gamji.

About andiya

Check Also

ABU to confer Honorary Degrees on Ngozi Okonjo-Iweala, Sheikh Sharif Ibrahim Sale

  . . . At its 44th Convocation billed for 25th January, 2025     …

Leave a Reply

Your email address will not be published.