Home / Labarai / An Kama Wani Kwarto A Jihar Kebbi

An Kama Wani Kwarto A Jihar Kebbi

Wata babbar kotun Gwamnatin tarayya da ke a Unguwar Nasarawa birnin Kebbi, Jihar Kebbi, ta mika wani mutum mai shekaru 24 mai suna Abubakar Garba, saboda aikata wani aiki da ya yi shigar mata sanye da hijab ya shiga gidan makwabcinsa da nufin ya yi wa matar Fade.
Lamarin dai ya faru ne a unguwar Asarara, cikin karamar hukumar Birnin Kebbi.
Jami’an yan sands ne suka kama mutumin bayan da aka kai masu korarin faruwar lamarin, wanda mai gidan Aliyu Hakimi ya kai koke da abin ya faru cewa ya zargi Abubakar Garba Garba shiga cikin gidansa inda ya yi shigar mata da nufin ya yi lalata da matarsa.
Amma sai matar mai suna Hauwa Aliyu, taki amincewa da shi kuma nan take ta nemi taimako daga makwabta abin da ya yi sanadiyyar kama Abubakar Garba.
A cikin bayaninsa Abubakar Garba ya amince da aikata laifin amma ya roki kotu da ta saukaka masa a game da laifin.
 Babban Alkalin kotun Mu’awaya Shehu Birnin Kebbi ya mikawa Yan sanda mai laifin a wurinsa zuwa sati mai zuwa lokacin da za a yanke hukuncin karshe.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.