Home / Labarai / Gidauniya Continental Ta Tallafawa Mabukata A Karamar Hukumar Rimi

Gidauniya Continental Ta Tallafawa Mabukata A Karamar Hukumar Rimi

Imrana Abdullahi
Gidauniyar Continental ta raba wa mabukata kayan Azumi na sama da naira miliyan shida a karamar hukumar Rimi.
Da yake jawabi shugaban Gidauniyar Alhaji Salisu Mamman Continental, ya bayyana cewa sun raba kayan ne domin su taimakawa  al’umar Karamar hukumar Rimi, musamman ma a cikin irin wannan yanayi da ake ciki.
 Ya bayyana cewa kafin wannan Shirin dama, sun kaddamar da wani shiri na taimakawa Al’umma inda za su ba mata dubu daya naira dubu Goma-Goma sannan kuma gidauniya za ta ba dalibai dari bakwai naira dubu Goma-Goma.
A jawabin nasa ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba da zaran wannan annoba ta yi sauki za su ci gaba da wadannan shirye shiryen.
Kayan da wannan kungiya ta raba sun hada da Buhunan Gero 105 wanda kiyasin kudinsu ya kama naira miliyan Daya da dubu dari buyu da Bakwai da dari Biyar (N1207500)
Sai kuma buhun  masara 105 Wanda shima kudinsa suka kama miliyan daya da dubu dari biyu da bakwai da dari biyar (N1207500)
Sai kuma katan din Taliya dari da biyar wanda kudinsu suka kama dubu dari uku da hamsin da Bakwai (357000).
Gidauniyar ta Kuma bayar da Naira Miliyan daya da dubu dari hudu (1,400, 000) ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na karamar hukumar Rimi.
Sai kuma sama da miliyan daya ga Limamai da Iyayen kasa na karamar hukumar Rimi.
Haka kuma an ware naira dubu Talatin N30,000 domin jigilar kayan zuwa mazabu Goma da ke karamar hukumar Rimi.
Haka kuma an ba shugabannin jam’iyyar a matakan karamar hukuma da mazabu kudin sayen sikari da Gero.
Jimmilla baki daya shugaban wannan gidauniya ya bada tallafin sama da naira miliyan Shidda.
Taron ya samu halartar duk wani mai kishin karamar hukumar Rimi wadanda suka hada da Babban Daraktan hukumar kula da gyaran hanyoyi ta jihar Katsina Engr. Surajo Yazid Abukur da Hon Nasiru Ala Iyatawa da Hon Gambo Abdukadir da sauran Iyaayen kasa da masu kishin karamar hukumar Rimi.

About andiya

Check Also

APC RELOCATES TO NEW STATE HEADQUARTERS IN GUSAU, ZAMFARA

The Zamfara State chapter of the All Progressives Congress APC has today relocated to its …

Leave a Reply

Your email address will not be published.