Home / Labarai / Hukumar Aikin Hajjin Nijeriya Ta Karyata Batun Kujeru Dubu 50

Hukumar Aikin Hajjin Nijeriya Ta Karyata Batun Kujeru Dubu 50

Hukumar Aikin Hajjin Nijeriya Ta Karyata Batun Kujeru Dubu 50
Mustapha Imrana Abdullahi
Kamar yadda hukumar aikin Hajjin tarayyar Nijeriya ta fitar da wata sanarwa cewa wata sanarwar da ake ta tallatawa a kafar yada zumunta ta zamani ta “Instagram” da kuma kamar yadda sanarwar ta bayyana mai yuwuwa ana yada wannan bayani a wasu kafafen sadarwa na zamani cewa a karshe Nijeriya ta samu kujeru dubu 50 domin aikin Hajjin bana 2021, hijiriyya 1442 wato bayan hijira, cewa tallar karya ne.
Tallar na yin kira ga maniyyat aikin Hajjin Bana cewa su ajiye kudinsu a yau domin su samu kujerar aikin Hajjin.
A saboda haka ne hukumar kula da aikin Hajji ta kasa ke sanar da jama’a cewa wannan sanarwa ba gaskiya ba ce.
Domin kasar Saudiyya har yanzu ba ta tuntubi hukumar aikin hajjin Nijeriya ba a kan duk wanibtsarin gudanar da shirin aikin Hajjin na shekarar 2021, babu kuma wata magana mai kama da warewa hukumar kujerun aikin Hajjin, matsayin Nijeriya kasa da jama’arta suke zuwa kasar Saudiyya domin sauke farali.
Saboda haka ake sanarwa da jama’a cewa a duk lokacin da irin wannan sanarwa ta samu hukumar NAHCON ba za ta yi kasa a Gwiwa ba wajen yi wa jama’a bayani da kuma rabar da kujerun ga jihohi kamar yadda ya dace.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.