Home / Labarai / Jami’an Tsaro Sun Samu Nasarar Hana Sace Mutane A Ikara Da Igabi

Jami’an Tsaro Sun Samu Nasarar Hana Sace Mutane A Ikara Da Igabi

Jami’an Tsaro Sun Samu Nasarar Hana Sace Mutane A Ikara Da Igabi
Mustapha Imrana Abdullahi
Tsakanin daren jiya Asabar da kuma wayewar gari wadansu mutanen da ake zargin cewa yan bindiga ne suka kutsa kai cikin makarantar sakandare ta Gwamnati da ke Ikara, a karamar hukumar Ikara cikin Jihar Kaduna, inda suka yi kokarin tsarewa da dalibai.
Kwamishinan kula da harkokin cikin gida da tsaro na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai a Kaduna.
Amma cikin ikon Allah sai daliban suka yi amfani da irin dabarun tsaron da aka Koyar da su, nan da nan suka ankarar da jami’an tsaron da suke a wannan yankin. Jami’an tsaron da suka hada da Sojoji, Yan Sanda da kuma masu aikin tsaron sa kai nan take suka je makarantar suka tunkari wadanda ake zargin, wanda hakan ya Sanya dole suka ranta a na kare.
Kwamishina Samuel Aruwan, ya ci gaba da cewa a halin da ake ciki jami’an tsaron Soja da yan Sanda suna can suna bin sawun yan bindigar.
Bayan mahukuntan makarantar sun kammala kidayar dukkan daliban sun tabbatar da cewa dukkan dalibai dari 307 suns nan ba wanda ya salwanta. Domin an samu nasarar hana yan bindigar aiwatar da kudirinsu kuma daliban na nan dai-dai ba wata matsala.
Kuma a wajen kauyen Ifira da ke karamar hukumar Igabi duk a cikin Jihar Kaduna, wadansu Yan bindiga sun yi yunkurin kai hari a rukunin gidajen kwanan manyan ma’aikata na filin Jirgin Sama da ke Kaduna. Nan ma wadanda suka kai harin ba su samu nasara ba domin jami’an tsaron Sojan Sama da na Sojan Kasa nasarar tarwatsa maharan baki daya wasu da yawa sun tsere tare da raunuka a jikinsu.
Gwamnatin Jihar Kaduna tana godiya game da irin yadda jami’an tsaro suka aiwatar da aikinsu inda suka samu nasarar tserar da dalibai 180 a  makarantar Koyar da harkokin Noma da Gandun Daji da ke Afaka. Wanda hakan an ji a bakin daliban da aka samu nasarar tseratarwa da sula bayyana hakan da bakinsu.
Gwamnatin Jihar Kaduna kuma na mika godiya ga jami’an tsaron Soja,Yan Sanda da jami’an Yan Sandan Farin kaya, wanda sakamakon aikinsu sun hana Yan bindigar tsarewa da wadannan dalibai 180 da muka lissafa a sama.
Gwamnatin Jihar Kaduna na gayawa duniya cewa ana nan kan kokarin ganin a ceto daliban da aka kwasa a makarantar da ke Afaka cikin koshin lafiya, as kuma a samu tsarin samun bayanai da harkokin tsaro domin hana ci gaba da samun matsalar tsaro a cibiyoyin ilimi.
A matsayinmu na Gwamnati shi ne tabbatar da an dawo da daliban da aka rasa da kuma hana faruwar hakan nan gaba,kuma za mu ci gaba da yi wa jama’a bayani a kan yadda lamarin yake gidana a nan gaba domin Gwamnati ba za ta bar mutane a cikin duhu ba.

About andiya

Check Also

Samar Da Tsaro Sai Kowa Ya Bayar Da Gudunmawarsa – Kaftin Joji

….A koma ga masu unguwanni, dagatai da hakimai Kaftin Muhammad Joji ya bayyana cewa lallai …

Leave a Reply

Your email address will not be published.