AN NADA DOKTA SULEIMAN SHU’AIBU DARAKTA JANAR TINUBU VANGUARD NA JIHAR ZAMFAR
…Shinkafi Ta Mamuda Ce, Shi Kowa Yake Ma Biyayya
DAGA IMRANA ABDULLAHI
TSOHON Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi, ya tabbatar da nadin Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, a matsayin Darakta Janar na kungiyar Tinubu Vanguard na Jihar Zamfara.
Mamuda Aliyu ya bayyana hakan ne a lokacin wata ziyarar da tawagarsa a garin Abuja hedikwatar tarayyar Najeriya.
A yayin ziyarar da suka kai garin Abuja, Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi tare da tawagarsa sun bayar da tabbacin ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga duk kokarin da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Mamuda Aliyu Shinkafi yake jagoranta.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin dan takarar Shugaban karamar hukumar Shinkafi Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, lokacin da ya kai masa ziyara tare da tawagarsa a cikin gidansa da ke Unguwar Mai tama cikin birnin babban tarayyar Najeriya Abuja
“Hakuri da juri’arka ya sa a koda yaushe kake ci gaba a dukkan abubuwan da aka Sanya ka a gaba”.
A lokacin ziyarar tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ya bayyana Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, a matsayin dan kwamitin amintattun kungiyar Tinubu Vanguard ..
Tinubu Vanguard, kungiya ce da za ta karade ko’ina da ko’ina a duk fadin tarayyar Najeriya domin tabbatar da ci gaban Najeriya da jama’arta baki daya.
Da yake tofa albarkacin bakinsa tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi, ya bayyana Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi a matsayin jajirtaccen kuma wayayye da ke kokarin taimakawa al’umma baki daya, wanda dalilin hakan jama’a ke binsa a duk inda ya sa gaba.
“Duk inda ya Sanya gaba zaka ga babbar gayyace ta jama’a don haka muna fatan samun nasara a koda yaushe”.
Mamuda Shinkafi ya bayyana Dokta Suleiman Shu’aibu a matsayin jagoran Tinubu Vanguard” domin fadakarwa da kuma yayata tafiyar Tinubu da Shattima domin samun nasarar zaben shekarar 2023.