Home / Labarai / Zulum Ya Baiwa Marayun CJTF 300 Da Suka Mutu A Yakin Boko Haram Tallafin N300m

Zulum Ya Baiwa Marayun CJTF 300 Da Suka Mutu A Yakin Boko Haram Tallafin N300m

 

Daga, Sani Gazas Chinade, Maiduguri

 

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum  ya kaddamar da shirin bayar da tallafin karatu na naira miliyan dari uku domin tallafawa marayu 300 da iyayensu suka mutu a matsayin masu aikin sa kai karkashin ’yan banga da mafarauta ‘Civilian Joint Task Force (CJTF)’.

Wadannan Masu aikin sa kai CJTF na da hannu wajen yakar ‘yan Boko Haram da ISWAP kafada da kafada da sojojin Najeriya a jihar Borno.

Gwamna Zulum yayin jawabinsa a wajen kaddamar da taron, wanda aka gudanar a dakin taro na multipurpose na gidan gwamnati dake Maiduguri, ya ce Naira miliyan 300 an ware ne domin biyan duk wani bukatu na ilimi na marayu 300 a duk matakin karatunsu na farko, kafin a ci gaba da tallafawa a mataki na gaba.  ilimi.

Zulum ya yi alkawarin tallafa wa marayu a karkashin shirin tallafa wa jaruman Borno na shekarar 2020.

Tun kafin gudanar da wannan tallafi  a lokuta daban-daban, ya ba da tallafi ga masu sa kai a fagen daga da kuma iyalan abokan aikinsu da aka kashe a fadace-fadacen da aka gudanar tsakanin su da ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP.

Baya ga tallafin, Gwamna Zulum ya kuma amince da bada  tallafin inganta rayuwa na akalla N15m ga iyaye mata da sauran masu kula da marayu 300.

Kowacce daga cikin iyaye mata ko masu kula da su 300 sun sami Naira 50,000 tare da buhun shinkafa, buhun masara da kayan sawa.

A jawabansu daban daban, shugabannin  kwamitin da Zulum ya kafa domin zabar marayu 300, Barista Kaka Shehu Lawan da kwamandan rundunar OPHK Manjo Janar Christopher Musa sun yaba da wannan shirin na Gwamna Zulum.

Kaka Shehu wanda a halin yanzu shi ne dan takarar kujerar Sanatan Borno ta tsakiya a karkashin jam’iyyar APC a zaben da ke tafe na 2023, wanda a baya aka  nada shi a lokacin da yake kwamishinan shari’a wanda ma’aikatarsa ​​ke kula da al’amuran ‘yan sa kai ta hanyar sashen da ke kula da ‘yancin jama’a.

Haka kuma a yayin kaddamar da tallafin ga marayu 300 na masu aikin sa kai da aka kashe, Gwamna Babagana Umara Zulum ya sanar da karin kashi 35% na alawus alawus da ake biya a duk wata ga ‘yan sa kan.

A watan Yunin 2019 Zulum ya kara alawus din daga 15,000 zuwa 20,000 sannan ya canza tsarin biyan kudi daga tebur zuwa asusun mutum na banki wanda hakan ya sa biyan kudi cikin sauri.

Gwamna Zulum ya kuma amince da bada albashin wata guda kyauta a karshen shekara ga kowane mamba na kungiyar sa kai na CJTF. Don karfafa musu gwiwa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.