Home / KUNGIYOYI / Gwamna Matawalle Ya Gwangwaje Yan Kungiyar Shehi/ Matawalle Da Kyautar Motoci 17

Gwamna Matawalle Ya Gwangwaje Yan Kungiyar Shehi/ Matawalle Da Kyautar Motoci 17

….SHUGABANNIN MATAN PDP SUN KOMA APC A JIHAR ZAMFARA
Daga Imrana Abdullahi
Sakamakon nuna jindadi da kokarin ficewar da shugabannin matan jam’iyyar PDP reshen Jihar Zamfara suka yi yasa Gwamnan Jihar ya gana da shugabancinsu karkashin Madina Shehu sakamakon kokarin dawo wa APC da suka yi.
Hajiya Madina Shehu ce ta tabbatar da batun ficewar daga PDP zuwa APC a ranar Alhamis a garin Gusau, babban birnin Jihar.
.Bayan tattaunawa da Gwamna Muhammad Bello Matawalle a Gusau, nan da nan sai ta bayyana batun ficewa daga PDP zuwa APC.
“Na bayyana ficewa saga PDP zuwa APC tare da dukkan shugabannin mata da ke kananan hukumomi Goma sha hudu (14), na Jihar Zamfara, inda ta bayyana matsalar rashin kyakkyawan shugabanci a matsayin matsalar da ta haifar da hakan”, Inji Madina.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Gwamna Matawalle, ya bayyana matakin da Madina Shehu ta dauka a matsayin abin da suke maraba da shi a jam’iyyar APC inda ya ce hakika akwai wadansu jama’a da dama da za su fice daga PDP zuwa APC mai albarka, a kwanan nan da suka hada da shugabanni a PDP
Gwamna Matawalle ya kuma karbi bakuncin yayan sananniyar kungiyar da ke yada manufofin Matawalle da tsohon Gwamna Shehi a a Jihar Zamfara baki daya.
Kungiyar mai suna “Matawalle/ Shehi Amalgamated Mobilisation Group” (MASAMOG) duk Gwamnan ya gana da du ne a ranar Alhamis.
Kuma wani abin farin ciki kuma Gwamnan ya bayyana bayar da kyautar motoci 17 ga yayan wannan kungiyar.
“Motoci kirar Bus guda biyu na shugabancin kungiyar ne an kuma bayar da wata kuma ga bangaren mata na kungiyar.
Motoci 14 kirar Fijo 406 an bayar da su ne ga Kodinetocin kungiyar a kananan hukumomi 14 na Jihar”, kamar yadda aka bayyana.
Gwamna Matawalle ya kuma yi alkawarin ci gaba da Tallafawa wannan kungiya, kasancewar a halin yanzu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun zama Tsintsiya madaurinki daya su na tare da Juna ba tare da wani bambanci ko tashin tashinar siyasa ba, a koda yaushe ana kokarin samun nasarar APC ne a duk fadin Jihar baki daya.
Sai Gwamnan ya yi Kira daukacin masu ruwa da tsaki, Mambobi da dukkan magoya baya a cikin Jihar da su kara dunkulewa a wuri daya domin yin aikin samun nasarar jam’iyyar a shekarar 2023 mai zuwa.
Tun da farko shugaban kungiyar, Alhaji Ibrahim Dan Maliki,bayyana Gwamna Matawalle da tsohon Gwamna Abdul’Aziz Yari ya yi a matsayin wadansu ginshikai masu kwarin gaske a cikin Jihar.
Ya ce an kafa wannan tafiyar ne domin samun gyara tsakanin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC ta yadda kwalliya za ta biya kudin Sabulu.
“Muna aiki ne domin tabbatar da samun komai ya ta fi dai dai a tsakanin shugabannin APC a Jihar Zamfara da nufin samun nasarar zaben 2023”, Inji Dan Maliki.

About andiya

Check Also

NTI in Collaboration with UNESCO TRAINS 250 Teachers on HIV Education, Family Life

By; Imrana Abdullahi The Director and Chief Executive of NTI, Prof. Musa Garba Maitafsir said …

Leave a Reply

Your email address will not be published.