Related Articles
Daga Imrana Abdullahi
Alhaji Bashir Sa’idu Gwammaja, wani na hannun daman shugaba Muhammadu Buhari ne kuma dan kasuwa ya bayyana cewa mantuwa ce a game da irin abin da ya faru a baya na rashin kwanciyar hankali da matsalar tsaro scan baya.
Alhaji Gwammaja ya ce in ban da matsalar mantuwa ta yaya har wasu za su rika cewa wai ba a samu ci gaba ba a kan irin abubuwan da ke faruwa
A can baya da koda masu zuwa masallaci da kuma yin Sallah dole sai an yi layi kafin shiga masallatai inda za a yi Ibada, kuma idan ana yin Sallar ma sai an raba wasu na gabatar da Sallah wasu kuma na tsaro don kada a kawo hari.
To amma a yanzu fa ai an samu ingantaccen canji saboda babu irin wancan matsalar da ta ke faruwa a baya, shin wannan na ci gaba ba ne.
“Ku duba fa ada can idan mutum ya fito daga gidansa shinge shingen jami’an tsaron da ake wuce sun yi wa jama’a yawa, amma a yanzu fa ai ba irin wadannan shigayen
An dai yi lokacin da sai mutum ya sauka daga kan Keke ko Babur na hawa ya gungura kafin ya wuce shingen jami’an tsaron da aka saka a kan tituna a cikin garuruwan jama’a.
“Ko wannan matsalar da ake kama mutane ana karbar kudin fansa duk arzikin da ake da shi ne ya jawo wannan, saboda akwai dimbin arziki a shimfida a cikin filin kasar da Allah ya bamu shi yasa wasu manya batagari suke hada kai da wasu daga kasashen Ketare ana taste arzikin”.
Ni a matsayi na na dan Najeriya mai kishin jama’a ina kira ga kowa da a ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwamnatin Muhammadu Buhari domin ya samar da taare tsare masu yawa a matsayinsa na mai kishin kasa tare da mutanen ta.