Home / News / Ayu Zai Iya Kai PDP Ga Nasara, Mutum Ne Mai Basira Shugaba Ne Mai  Biyayya: Yan PDP Arewa Maso Yamma

Ayu Zai Iya Kai PDP Ga Nasara, Mutum Ne Mai Basira Shugaba Ne Mai  Biyayya: Yan PDP Arewa Maso Yamma

Daga Imrana Abdullahi
Gamayyar kungiyoyi kwararru na jam’iyyar PDP masu kokarin tabbatar da zaman lafiya ( PDPCUP) sun bayyana shugaban jam’iyyar PDP na kasa Dokta Iuorchia Ayu, a matsayin jajirtaccen mutum wanda keda kwarewar da zai kai jam’iyyar ga Tudun muntsira na nasara.
Zai kuma iya fitar da jam’iyyar daga halin da take ciki na kalubalen da take fuskanta kafin zaben shekarar 2023.
Alhaji Muhammad Dan’Auta, shugaban gamayyar kungiyoyin, ya bayyana hakan a wajen taron masu ruwa da tsakin jam’iyyar da ya gudana a Kaduna.
Alhaji Dan Auta ya ce shugaban jam’iyyar, Dokta Ayu ya cancanci dukkan goyon baya daga yayan jam’iyyar musamman ma idan aka yi la’akari da irin ayyukan da ya aiwatar a baya, mutum ne mai natsuwa da aiki tukuru kuma dan siyasa mai dimbin basira da ya saudar da kansa a lokuta da dama wajen tabbatar da hadin kai da inganta al’amura a kasa duk da irin kalubale daga wasu yan Boko da suke ganin su masu ilimi ne.
“Tsananin natsuwa da kokarin yin haba haba da jama’a ya haifar wa da jam’iyyar PDP samun ci gaba, duk da irin matsalolin kushe da wadansu kalaman da ake yi ga shi kansa shugaban PDP na kasa duk da hakan alamu ne da ke nuni da cewa yan Najeriya ba za su yi kuka ko Dana sanin zabar PDP ta dawo a kan karagar mulki ba.Shi da shugaba ne da ke kokarin kawo wa kasa da jama’ar ci gaban da kowa ke bukatar a samu ingantawar al’amura a kasa”.
Kungiyar ta yi alkawarin yin aiki tukuru domin yayata Gwarzon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da sauran yan takara na jam’iyyar a yankin jihohin arewacin Najeriya baki daya da nufin samun sahihiyar ingantacciyar nasarar jam’iyyar PDP.
A game da batun takarar Atiku, yayan kungiyar sun ce, idan aka zabi Atiku da Okowa a matsayin shugaba da mataimaki, suns da dukkan karfin gudanar da aikin da ake bukata su warware kalubalen da ake fuskanta su kuma yi wa kowa adalci ta hanyar yin dai- daito ga yan Najeriya baki daya.
Gwamnatinsa za ta kasance ta dukkan yan Najeriya ne ba wai yanki,addini ko wasu masu batutuwan kabilanci ba.
“Muna da yakinin cewa yan Najeriya za su amince da Atiku su kuma bashi dama ta hanyar fitowa kwansu da kwarkwatarsu, su zabi jam’iyyar PDP su kuma tsare abin da sula zaba bayan sun gudanar da zabensa a ranar zabe”.
Yan Najeriya ya dace su dawo daga Rakiyar wadannan yan siyasar da suka kasance sun Kagara su kawo matsalar rashin hadin kai ta fuskar kabilanci,addini da kuma bambancin yanki.Kalamansu za su iya haifar da matsala ga Dimokuradiyyar da ake yi da kuma matsalar rashin zaman lafiya.
Yin amfani da wadansu kalamai, jaguar da rashin jituwa da batun tsananin addini ba za su taimaka wajen warware matsalar siyasa, sai dai kawai su kara haifar da batun batanci da kuma kara Muammar yanayin harkokin siyasa.
Malam Dan’Auta ya ce daya daga cikin dalilan da suka Sanya suka yi wannan taron domin a samar da mafita game da wadansu kalubale a kuma tattauna a tsakanin Juna da za su taimakawa jam’iyyar ta fuskar ci gaba da hadin kai da nufin samar da ci gaba a yankin arewacin Najeriya.

About andiya

Check Also

NTI in Collaboration with UNESCO TRAINS 250 Teachers on HIV Education, Family Life

By; Imrana Abdullahi The Director and Chief Executive of NTI, Prof. Musa Garba Maitafsir said …

Leave a Reply

Your email address will not be published.