Daga Imrana Abdullahi

…Jerin sunayen sun hada da mata biyu da maza 17.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya mika sunayen mutane 19 ga majalisar dokokin jihar domin a tantance tare da amincewa da su a matsayin kwamishinoni da mambobin majalisar zartaswar jihar.
Kakakin majalisar dokokin jihar, Yusuf Falgore ne ya sanar da hakan a zaman majalisar a ranar Talata, yayin da yake karanta takardar bukatar gwamnan.
An bukaci wadanda aka nada su bayyana a gaban majalisar a ranar Laraba domin tantancewa da karfe 10:00 na safe.
Ga dai jerin sunayen nan;
1. Aminu Abdulsalam
2. Umar Doguwa
3. Ali Haruna Makoda
4. Abubakar Labaran Yusuf
5. Danjuma Mahmoud
6. Musa Shanono
7. Abbas Sani Abbas
8. Aisha Saji
9. Ladidi Garko
10. Dr. Marwan Ahmad
11. Engr. Muhd Diggol
12. Adamu Aliyu Kibiya
13. Dr. Yusuf Kofar Mata
14. Hamza Safiyanu
15. Tajo Usman Zaura
16. Sheikh Tijjani Auwal
17. Nasiru Sule Garo
18. Haruna Isa Dederi
19. Baba Halilu Dantiye