Daga Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya amince da nadin Samuel Aruwan a matsayin shugaban hukumar kula da babban birnin jihar Kaduna (KCTA).
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Muhammad Lawal Shehu Babban Sakataren Yada Labarai da aka rabawa manema labarai
Kafin nadin nasa dai Aruwan shi ne tsohon kwamishinan majagaba na ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna.
Ya kammala karatunsa na Mass Communication, ya shafe shekaru Goma ya na aiki a kafafen yada labarai daban daban kafin ya shiga aikin gwamnati a shekarar 2015.
Ya na da gogewa da sanin makamar magance rikice-rikice da gudanar da mulki, kasancewarsa ya taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi da yakin da ake yi da ta’addanci da ‘yan fashi a Arewacin Najeriya.
A yayin da yake taya Aruwan murnar nadin nasa, Gwamnan ya bukace shi da ya yi amfani da fasahar aikin da yake da ita, da kuma zurfin iliminsa na gudanar da mulki da gudanar da mulki domin daukaka babban birnin Kaduna. Ya yi fatan Allah ya yi masa jagora a sabon aikinsa.